27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Hotunan yadda aka gudanar da bikin nadin sarautar Amaechi a garin Daura

LabaraiHotunan yadda aka gudanar da bikin nadin sarautar Amaechi a garin Daura

Mahaifar Buhari wato Daura ta cika da annashuwa yayin da aka ba wa Rotimi Amaechi saurautar gargajiya, bidoyon da ya bazu a yanar gizo ya nuna lokacin da yake tafe a kan doki misalin karfe 11:11 na safiyar ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairun 2022, Legit.ng ta ruwaito.

Sarkin Daura, mai martaba Faruk Umar Faruk, ya nada Rotimi Amaechi a matsayin ‘Dan Amanar Daura a ranar Asabar. Sarautar gargajiyar mai taken ‘Dan amanar masarautar Daura da aka ba shi yana nuni da yaba wa kokarin Amaechin wajen kawo ci gaba ga masarautar.

Yayin nuna cancantar mukamin ga Amaechi, Sarkin ya bayyana dalilin da yasa ya ba shi sarautar kawai saboda matukar kwazon sa ne.

rotimi
Hotuna da bidiyon yadda aka gudanar da nadin sarautar Amaechi a garin Daura

Jihar Katsina– farin ciki ya karade garin da aka haifi shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, yayin da minista kula da zirga-zirgi, mai girma Chibuike Rotimi Amaechi ya amshi sarautar gargajiyar.

Minista Amaechi ya nuna matukar godiyar sa ga mutanen Daura na ba shi sarauta mai taken “Dan Amanar Daura,
Inda ya wallafa a shafin sa na Twitter:

“Ina godiya ga Sarki, masarautar da mutanen Daura saboda wannan babbar karramawa ne, nada ni a matsayin Dan Amanar Daura. Ina godiya gare ku da amsa na a matsayin amintaccen da kuma abokin kawo ci gaban kasar mu.”

Ba Amaechi kadai aka nada ba, har da dan kasuwan nan, Alhaji Nasiru Halidu Danu, inda aka ba shi sarautar ” Tafida Babba Daura.

Sarkin, Dr Umar Faruk Umar, ya basu mukaman ne saboda yaba wa irin kokarin da suke yi wajen kawo ci gaba ga masarautar, Katsina da kasa baki daya. Bidiyon ya nuna Amaechi akan doki bayan an nada shi.

Martanin ‘yan Najeriya kan nadin Yusuf Buhari sarautar Talban Daura

‘Yan Najeriya da dama sun mayar da martani, bayan BBC Hausa ta wallafa hotunan dan shugaban kasa, Yusuf Buhari wadanda aka nada shi sarautar Talban Daura.

Labarun Hausa ta yi dubi akan tsokaci da dama wadanda ‘yan Najeriya su kayi, duk da wasu sun yi suka akan nadin sarautar yayin da wasu su ka yi murna tare da masa fatan alkhairi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Punch

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe