36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Aure arha gare shi, sai dai idan dan karya ne kai: Hotunan auren matashin da ya kashe N20,500

LabaraiAure arha gare shi, sai dai idan dan karya ne kai: Hotunan auren matashin da ya kashe N20,500

A ranar Lahadi, misalin karfe 11:25 na safiyar 6 ga watan Fabrairu, 2022
Wani dan Najeriya mai suna Ani Nnamdi Chris, ya angwance da matar sa yayin da suka yi kwarya-kwaryan taro wanda suka gabatar a sirran ce, legit.ng ta ruwaito.
Yayin wallafa hotunan shagalin da ya guduna a 4 ga watan Fabrairu, Chris ya ce, gaba daya abinda ya kashe na bikin N20,500 ne.
Mutumin cikin alfahari ya kara da bayyana yadda ya tarbi mutane 10 kacal wadanda suka hada da shi da matar tasa, inda ya ce aure bashi da tsada ya danganta da karfin ka
.

wedding


Wani sabon ango dan Najeriya mai suna Ani Nnamdi Chris ya ba wa duniya mamakin yadda ya angwance da masoyiyar sa, inda suka gabatar da wani dan kwarya-kwaryar taron sirri.
Chris ya wallafa hotunan dan karamin shagalin bikin, wanda ya gabata a 4 ga watan Fabrairu a shafin sa na Twitter, inda ya bayyana gaba daya abinda ya kashe a N20,500 inda yace ya biya N15,500 a matsayin kudin rijista a kutu, inda ya bada N5,000 ga mai rigistar ya sha ruwa.
A cewar Chris aure babu tsada, dan kwarya-kwaryar taron ya biyo bayan daurin auren a kotu ne, inda ya kunshi mutane 10 kacal duk da shi da matarsa.
Ga tsokacin jama’a a karkashin wallafar tasa;

Sammygyang ya ce: ” Kana da dabara. Ina taya ka murna! Kayi wa auren ka tanadi ba biki ba. Mutane da yawa suna almubazzaranci a bukukuwan su suke yi duk don su birge tarin mutanen da basa kaunar su. Amma idan auren ya lalace, kashi 80 cikin 100 na mutanen sune zasu fara gulmarsu a shagon aski da gidajen giya.”
@emelda_ ani ya rubuta: “Kawu na Nnamdi, kamar yadda naji dadin abinda kayi, baka bada cikakken labarin ba. Kada kasa wadan nan kananan yaran su yi tunanin dubu 30 zata ishe su aure. ” Yanzu, baka bamu labarin yadda shagalin bikin al’adan ya kaya ba. Ina da tabbacin ka biya sadakin ta.”
@ejyvik yace: ” Ina jan kunnen aboki na da matar sa da suka sa ni na biya dubu 160 na ankon da ban sa ba, idan suka yi kuskuren nuna sun gaji da auren, su fara tunanin biya na kudi na har da riba, Ubangiji ya albarkaci gidan auren ku.

Budurwa ta kwashe saurayinta da mari har sau 2 saboda ya nuna yana son aurenta a bainar jama’a

Wani saurayi da yayi yunkurin bawa budurwar shi mamaki wajen neman aurenta, amsar da ta dawo mishi da ita ba ta yi masa dadi ba, yayin da budurwar ba wai taki amincewa ba ne kawai, ta mayar da martani da duka ne.

Wani mai amfani da shafin sadarwa na Twitter, mai suna @EazyKel_who yaa wallafa bidiyon yadda wannan lamari ya faru a shafinsa, inda ya caccaki mutumin kan dalilin da ya sanya ya nemi auren budurwar tashi a bainar jama’a.

Neman auren bai yiwa saurayin yadda yake so ba

Yayin da aka nuno saurayin ya durkusa a gaban budurwar, ga kuma cake a kan tebur inda budurwar take zaune, an gano budurwar ta tashi tsaye ta kwashe shi da mari, inda take tambayar shi dalilin da ya sanya shi ya zo wajen.

Duk da kokarin da mutane suka din yi wajen ganin sun shawo kan budurwar, budurwar ta kara kwashe saurayin da mari a karo na biyu a yayin da yake tsugunne a gabanta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe