34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ƙasar Faransa ta kafa wata sabuwar hukuma wacce za ta sauya fasalin addinin Musulunci a fadin kasar

LabaraiƘasar Faransa ta kafa wata sabuwar hukuma wacce za ta sauya fasalin addinin Musulunci a fadin kasar

Ɗumbin musulmai ma su faɗa aji a ƙasar Faransa, gwamnati ta zaɓo domin kasancewa cikin taron kafa hukumar musulunci. Waɗanda ke sukar lamarin na ganin cewa wannan wani yunƙurin shugaba Emmanuel Macron ne na samun goyon baya.

Ƙasar Faransa za ta gudanar da taron ƙoli na farko domin kafa wata sabuwar hukuma ranar asabar. Taron zai mayar da hankali ne wajen sauya rayuwar musulmai a ƙasar da kuma cire tsatstsauran ra’ayi daga cikin addinin musulunci.

Mahalarta taron waɗanda za su haɗu a birnin Paris, sun haɗa da malaman addini, mutane maza da mata waɗanda za su taimaka wajen jagorantar al’ummar  Musulmai mafi girma a yammacin nahiyar Turai

Sun haɗa da limamai, masu faɗa aji daga kungiyoyin jama’a, manyan mutane da kuma manyan ‘yan kasuwa.

Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron. Hoto daga Google

Ƙasar Faransa ta sha hare-haren ta’addanci a baya

Har yanzu ƙasar Faransa tana cigaba da jin raɗaɗin hare-haren masu tsatstsauran ra’ayin addinin Islama wanda ya hallaka mutane da yawa a shekaru 10 da su ka wuce.

Har yanzu ƙasar ta kasa fahimtar yadda akayi ɗaruruwan musulman ƙasar su ka shiga ƙungiyar ISIS a ƙasar Syria da Iraq.

Sai dai waɗanda ke sukar lamarin, na ganin cewa wannan kawai wani yunƙuri ne na shugaba Emmanuel Macron wajen ganin jam’iyyar sa ta samu goyon baya ta hanyar juya al’ummar musulmai.

Ko menene ayyukan hukumar?

Hukumar za ta riƙa gudanar da tarurrukan ta a duk shekara, sannan za ta raba ayyukanta zuwa gida huɗu kamar irin shirin ƙasar Jamus na Deutsche Islam Konferenz (DIK).

Ayyukan hukumar za su mayar da hankali wurin horas da limamai, malaman da aka ɗauka aiki a gidan kaso, asibitoci da soji, sannan kuma da samar da tsaron masallatai da kuma hana nuna wariya akan musulmai.

Musulmai na shan tsangwama a ƙasar Faransa

Musulmai a ƙasar Faransa sun sha korafin shan tsangwama a rayuwar su ta yau da kullum, inda su ka nuna cewa tsangwamar ta ƙaru sosai bayan kai wasu hare-haren ta’addanci.

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: An sanya sabuwar doka ta hana sanya Hijabi a kasar Faransa

Sabuwar doka da ake shirin kaddamarwa a kasar Faransa ta hana mata sanya Hijabi a cikin jama’a na kokarin yada kyamar Musulunci a cikin al’ummar kasar.

A cewar gwamnatin ta kasar Faransa, sabuwar dokar an sanya ta ne domin shawon kan hadarin raba kan al’umma ta yadda sanya Hijabin yake ware Musulmai da sauran al’umma, yayin da majalisar dokokin kasar tuni ta rattaba hannu akan wannan sabon kuduri.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe