24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Aliko Dangote ya sha alwashin abinda zai yi, idan har Najeriya ta kasa buge Ghana a wasan da za su buga na cin kofin duniya

LabaraiAliko Dangote ya sha alwashin abinda zai yi, idan har Najeriya ta kasa buge Ghana a wasan da za su buga na cin kofin duniya
  • Biloniya Aliko Dangote ya sha alwashin ƙin kallon gasar cin kofin duniya idan har Najeriya ta kasa buge ƙasar Ghana domin samun gurbin zuwa gasar
  • Ƙasashen biyu na yankin Afrika ta yamma za su fafata domin samun gurbin zuwa gasar wacce za’a yi bana a ƙasar Qatar
  • Zakaran da ya lashe wasannin biyu shine zai wuce zuwa gasar wacce za ta gudana a watan Nuwamban 2022 a ƙasar Qatar

Aliko Dangote, wanda yafi kowa kuɗi a nahiyar Afrika, ya bayyana cewa ba zai kalli gasar cin kofin duniya ba idan har ƙasar sa Najeriya ta kasa buge ƙasar Ghana domin samun gurbin zuwa gasar. Jaridar Sports Brief ta ruwaito.

Najeriya za ta fafata da ƙasar Ghana a gida da waje a watan Maris domin samun gurbin zuwa gasar wacce za ta gudana cikin wannan shekarar a ƙasar Qatar.

Aliko Dangote ya bayyana muhimmancin gasar a wajen sa

Yayin da ake shirye-shiryen wasan, Aliko Dangote wanda yaje filin da Najeriya za ta amshi baƙuncin ƙasar Ghana, ya bayyana yadda muhimmancin gasar kofin duniyar ta ke a wajen sa da kuma ‘yan Najeriya.

Ba ni kaɗai gasar ta ke muhimmanci a gare ni ba, tana da muhimmanci a dukkanin mu da mu ke wannan waje. Wannan shine abin alfaharin mu a matsayin mu na ‘yan Najeriya.” a cewar sa.

Idan har Najeriya ta kasa samun gurbin zuwa gasar, to lallai ba zanje ba.”

Aliko Dangote
Aliko Dangote ya nuna muhimmanci wasan kofin duniya a gun shi

Ƙasashen biyu ba suyi ƙwazo ba a gasar AFCON

Ƙasashen guda biyu ba suyi abin azo a gani ba a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta bana, inda ƙungiyar Black Stars ɗin na ƙasar Ghana su ka kasa wuce zagayen farko, ita kuwa Super Eagles ta sha kashi a zagaye na gaba.

Ƙungiyar Black Stars ta ƙasar Ghana ba ta samu halartar gasar ba wacce aka gudanar a ƙasar Rasha a shekarar 2018, inda yanzu su ke fatan zuwa gasar da zaa yi a ƙasar Qatar.

Sai dai, su na da Najeriya wacce ta samu halartar gasar har sau 6 a gaban su akan hanyar su ta zuwa gasar ta bana.

Ana yiwa ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya barazanar kisa saboda sun sha kasa a wasan AFCON

Korar Najeriya da ƙasar Tunusia tayi a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON), a zagaye na 16, babban abin takaici ne a wajen magoya bayan ƙungiyar.

Ba kawai ana fatan kungiyar Super Eagles tayi nasara kawai a wasan bane, amma ana yiwa ƙungiyar kallon wacce zata iya kaiwa har zuwa wasan ƙarshe a gasar inda ake sa ran zata goge raini da ƙasar Kamaru mai masaukin baki.

Dalilin samun wannan ƙwarin guiwar ya samo asali ne yadda tawagar tayi abun kirki a wasannin ta na ukun farko inda ta samu maki tara, sannan ta zura aƙalla kwallo biyu a kowane wasa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe