27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Budurwa ta kwashe saurayinta da mari har sau 2 saboda ya nuna yana son aurenta a bainar jama’a

LabaraiBudurwa ta kwashe saurayinta da mari har sau 2 saboda ya nuna yana son aurenta a bainar jama'a

Wani saurayi da yayi yunkurin bawa budurwar shi mamaki wajen neman aurenta, amsar da ta dawo mishi da ita ba ta yi masa dadi ba, yayin da budurwar ba wai taki amincewa ba ne kawai, ta mayar da martani da duka ne.

Wani mai amfani da shafin sadarwa na Twitter, mai suna @EazyKel_who yaa wallafa bidiyon yadda wannan lamari ya faru a shafinsa, inda ya caccaki mutumin kan dalilin da ya sanya ya nemi auren budurwar tashi a bainar jama’a.

Neman auren bai yiwa saurayin yadda yake so ba

Yayin da aka nuno saurayin ya durkusa a gaban budurwar, ga kuma cake a kan tebur inda budurwar take zaune, an gano budurwar ta tashi tsaye ta kwashe shi da mari, inda take tambayar shi dalilin da ya sanya shi ya zo wajen.

Duk da kokarin da mutane suka din yi wajen ganin sun shawo kan budurwar, budurwar ta kara kwashe saurayin da mari a karo na biyu a yayin da yake tsugunne a gabanta.

Daga baya kuma ta dauki wannan cake da ya kawo ta jefe shi da shi, hakan ya sanya kayan jikin shi suka lalace, duka dai saurayin yana tsugunne a gaban ta bai tashi ba.

Sharhin mutane kan wannan lamari

“Mata da yawa suna cewa wannan wasan barkwanci ne. Saboda sun ga yadda haka kawai mace ke zama bala’i ba tare da anyi mata komai ba.. Wannan abu ne da muke magana a kai a koda yaushe..”

@nathan_oji

“Gaskiya wannan wasan kwaikwayo ne. Na kasa yadda cewa wannan gaskiya ne. Saboda mai yasa take marin shi shi kuma ya tsaya ya kasa yin komai. Sai dai ko idan abin ya daure masa kai ne.”

@realsabigurl

“Babu dalilin ci masa mutunci, za ta iya cewa aa.. wannan marin da take yi masa bai kamata ba kwata-kwata.. Idan taki amincewa shikenan ba wani damuwa.. amma inda matsalar take shine dalilin da ya sanya take marin shi. Babu alamun hankali a wannan abu.. ta yi sa’a saurayin bai canja mata ba a lokacin.

@Onye_Bolt

“Ta yi mini daidai, wasu mazan suna amfani da bainar jama’a ne su tilasta budurwa ta amince da su, koda bata da niyya.”

@Myppen002

“Idan har baka yi mata ihu a bainar jama’a, to kada ka nemi aurenta a bainar jama’a.”

Budurwa ta shiga tashin hankali, bayan ta gano saurayin da suka shafe shekara 5 suna soyayya ya shekara 7 da igiyar aure a kanshi ba ta sani ba

Wata budurwa mai amfani da kafar sadarwa ta Twitter ta hau shafinta ta bayyana halin da kawarta ta shiga bayan ta gano cewa saurayinta da suka shafe shekara biyar suna soyayya ya shekaraa bakwai da igiyar aure a kanshi ba tare da ta sani ba.

A cewar budurwar mai suna @Chrisssssy_Payn a shafinta na Twitter, kawarta ta gano cewa saurayinta yana da aure, bayan ya wallafa hotunan matarshi a WhatsApp yana su murnar cika shekara bakwai da yin aure.

Ya yiwa matarshi karyar daga ita ba wata mace a gabanshi

@Chrisssssy_Payn ta ce mutumin yayi ta koda matarshi a WhatsApp har yana gaya mata cewa ita kadai ce mace daya da yake so a rayuwar shi.

Da take bayyana yadda lamarin ya kasance a shafinta na Twitter, ta ce:

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe