27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Kamfanin kayan kwalliya sun bawa Sarauniyar kyau Shatu Garko mukamin jakadarsu a Najeriya

LabaraiKamfanin kayan kwalliya sun bawa Sarauniyar kyau Shatu Garko mukamin jakadarsu a Najeriya

Fitaccen kamfanin kayan kwalliya na Aspira ya bawa Sarauniyar Kyau ta Najeriya Shatu Garko, mukamin jakada a Najeriya, inda aka gabatar da taron a jihar Lagos…

Fitacciyar jarumar Nollywood, Adesua Etomi-Wellington, ta samu mukamin jakadar wani sabon kayan kwalliya, mai suna “Siri Beauty Soap”, na kamfanin Aspira dake Najeriya.

Haka kuma, Shatu Sani Garko, kyakkyawar budurwa ‘yar jihar Kano da ta samu nasarar lashe kambun Sarauniyar Kyau na shekarar 2021, ita ma an bayyana sunanta a cikin jakadun, wanda aka yi a Victoria Island, cikin jihar Legas.

Bayanin shugaban fannin kasuwanci na kamfanin

Shugaban sashen kasuwanci na kamfanin, San Tosh ya ce, wadanda aka bawaa mukamin jakadun sun cika duka sharuddan kamfanin Aspira ta fuskar gaskiya da gogewa a sana’o’in da suka zaba.

Ya bayyana cewa, kamfanin na su yaa bibiyi yadda matasan Najeriya ke gudanar da ayyukansu a Najeriya da kuma bangaren da suka fi yin shuhura, hakan ya sanya aka zabi Adesua Etomi-Wellington da kuma Shatu Garko a matsayin jakadun kamfanin.

A cewar shi, jarumar ta Nollywood tana daya daga cikin fitattun fuskoki a masana’antar fina-finai da nasarorin da ta samu a matsayin jarumar yana karawa matasa masu tasowa kwarin guiwa.

Sarauniyar Kyau Shatu Garko
Sarauniyar Kyau Shatu Garko

“Babu wani abu da zamu karu dashi don munce ta zama daya daga cikin fitattun fuskoki a Nollywood, kuma bayan haka nasarorin da ta samu a matsayinta na jaruma.

Abin ya bani sha’awa ganin har kamfani suna da shi a Kano – Adesua

Da take nuna farin cikinta kan wannan mukami da ta samu, Adesua ta ce:

“Na yi farin cikin nada ni a matsayin jakadar Siri. Ni mai kaunar mata ce da kuma kara musu kwarin guiwa akan kyawun halittar da suke da ita, ba tare da la’akari da yanayin jikinsu, girman su ko kuma kalar fatar su ba.

“Kowacce mace ta cancanci ta ji dadi. A lokacin da na gana da daraktocin Siri, sai na ji abin ya bani sha’awa ganin cewa suna da masana’antar su a Kano, Wannan dama ce mai ban mamakii dake nuni da cewa za a samar da ayyukaan yi a Najeriya,” ta kara da cewa.

Shatu Garko ta yabawa kamfanin da kuma kayan kwalliyar su

A na ta bangaren, Sarauniyar Kyau Shatu Garko, ta ce wannan sabon kayan kwalliya zai yi daidai da irin kayan da ‘yan Najeriya suke so, saboda an basu zabin da ya dace na kayan kwalliya da sabulu mai kamshi.

“Ina ganin wannan samfurin zai yi daidai da bukatun ‘yan Najeriya da yawa, saboda ba dole sai mutum yayi amfani da turare ba, don haka Siri zai zama zabin da mutane suka fi so,” in ji ta.

Kambun Sarauniyar Kyau ya riga ya hau kai na ‘yan bakin ciki sai dai su mutu – Shatu Garko

Kyakkyawar budurwar da ta lashe gasar Sarauniyar Kyau ta Najeriya da aka gabatar zango na 44, Shatu Garko, ta caccaki mutanen da suke zagin ta kan shiga gasar da ta yi saboda kasancewar ta Musulma.

Shatu Garko mai shekaru 18 a duniya, ta ce duk da ta san cewa makiya za su cigaba da magana kan wannan nasara da ta samu, amma kambun sarautar Sarauniyar Kyau ya riga ya hau kanta kuma babu abinda za ta iya yi akan haka.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata jaridar Labarun Hausa ta kawo muku rahoton yadda Kwamandan hukumar Hisbah Harun Ibn-Sina, ya ce rundunar su ta Hisbah za ta gayyaci iyayen Shatu Garko domin amsa tambayoyi kan dalilin da ya sanya suka kyale ‘yarsu ta shiga gasar Sarauniyar Kyau.

Gasar ta Sarauniyar Kyau an gabatar da ita a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 2021 a dakin taro na Landmark Center, dake cikin Victoria Island, cikin jihar Lagos.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe