34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Yadda miji ya banka wa matar sa wuta bayan ya gano ta siya kadara ba tare da sanin sa ba

LabaraiYadda miji ya banka wa matar sa wuta bayan ya gano ta siya kadara ba tare da sanin sa ba

Wata kotu da ke Akure a jihar Ondo ta saurari shari’ar yadda wani mutum mai shekaru 50, Daniyan Ojo ya garkame matarsa, Docas yayin da take bacci a dakin ta, inda ya banka wa gidan wuta. An samu labarin yadda matar ta sheka lahira bayan kwana uku da aukuwar al’amarin saboda irin mumanan kunan da tayi duk da irin kulawan da ta samu a asibiti.
Majiya daga ‘yan uwa ta bayyana dalilin da yasa mijin ya dauki mummunan matakin bayan ya gano matarsa ta siya wani kadara ba da izininsa ba, Vanguard ta ruwaito.

An gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu, inda ake zargin sa da banka wa dakin matar sa da kuma garkame ta a cikin daki a gidan su na layin Irese a kauyen Shagari da ke Akure.
Amma sai dai H.M Falowo wanda ya ke jagorantar tuhumar ya ce ana tuhumar sa da haddasa gobara, kisan kai da kin amincewa da laifin sa.
An zargi Daniyan da dode hanya guda daya da wacce al’amarin ya auku da ita za ta iya samu ta tsira (kofa) a lokacin da ya banka mata wuta, dan hanata guduwa.

ondo 1
Yadda miji ya banka wa matar sa wuta bayan ya gano ta siya kadara ba tare da sanin sa ba


Ganau wanda yake da kusanci da iyalin, Ajayi Ajiboye ya bayyana wa kotu yadda ya ji muryar mamaciyar tana neman agaji. Ya ce, “a lokacin da na isa farfajiyar, na gane dakin matar ne ke ci da wuta, sai na yi amfani da karfin na balle kofar da kafata.
Ya siffanta yadda matar ta babbake fiye da yadda za’a iya gane ta, yayin da ya garzaya makwabta neman agaji, inda suka zo don ceton rai, kuma suka wuce da ita zuwa asibiti don samun kulawa.
A cewarsa, “washe gari da safe, mai gidan hayan wanda ke makwabtaka dasu yazo gidan, inda ya samu kwalaban man fetur a watse kan gadon wacce ibtila’in ya auka mawa a wurare daban-daban na sakon dakin.”
Haka zalika,dan uwan marigayiyar, Adeniyi Samuel, ya shaida cewa, wanda ke kare kan san ya kai karar wadda al’amarin ya auku da ita, akan cewa ya ga takardar kadarar abun hawan da marigayiyar ta siya.
Ya bayyana yadda ya ari bakin ‘yar uwar sa ya bashi baki, amma bayan wasu kwanaki, wanda ake zargi ya kara kawo masa karar ta akan fuloti uku da ta siya, kuma tayi rijista da sunan ta.
Adeniyi ya tabbatar da cewa ‘yar uwar tasa ta fada masa dalilin ta na siyan kadarar da sunan ta saboda taji tsoron mijin zai iya sayar da su ba tare da izinin ta ba.

Ya bayyana yadda yayi sasanci tsakanin su, inda ya koma mazaunin sa, amma daga baya aka kirashi a waya ake shaida masa yadda wuta ta kama mazaunin su, wanda hakan yayi sanadiyyar babbakewar ‘yar uwarasa. Ya ce a lokacin da ya ziyarci marigayiyar a FMC, Owo, ta rattafa masa abun da ya auku lokacin da ta isa gida wanda tsabar babbakewar da tayi ne yayi sanadin shekawar ta barzahu.
A cewarsa, “hakan yasa yan sanda suka shiga al’amarin har suka damko wanda ke kare kansan, wanda ya tsere lokacin da al’amarin ya auku.” Yarinyar marigayiyar ta kara da bayyana yadda mahaifin nata ta ya shirya wa iyalin abincin dare, sannan ya shaida musu cewa zaije siyo fetur.
“Ban dade da tashi daga bacci ba lokacin da mahaifiyata ta dawo daga tafiya, inda daga bisani ta kwanta bacci. Sai dai hayaniyar motar da ta dauki mahaifiyata zuwa asibiti ce ta tadani daga bacci,” a cewar ta.

Wani makwabci, Igunsola Babatunde ya bayyana yadda yaji kururuwa a farfajiyar wanda ake tuhuma, wanda hakan yasa ya je don jin musabbabin kururuwar.
“Na sami sauran masu kula da gidajen hayan wajen, dukkan mu mun jiyo ihun matar, tana cewa ‘mijina ne musabbabin gobarar.’ Daga bisani wacceal ‘amarin ya auku da ita ta sheka lahira a asibitin saboda tsabar kunan da tayi.”
Sifeta Bayo Adaran ne ya mika al’amarin daga hukumar ‘yan sandan Okuta Elerinla zuwa ga hukumar bincike na jihar (SCID) don cigaba da binciken sirri, kuma yana cikin wadanda suka gudanar da binciken. Adaran ya kara da bayyana yadda ya ziyarci wajen da abun ya auku har ya damko wanda ake zargin.

Miji ya bawa matar sa kwaya ya gayyato abokin aikin shi ya yi mata fyade akan idon shi

An yanke hukuncin zama gidan kaso na shekaru 3 ga wani mutum bayan yayi yunƙurin yin fyade ga matar abokin aikin sa, wacce mijinta ya gayyace shi domin yin wannan ɗanyen aiki.

An faɗi wannan labarin mara daɗin ji ne a kotun ƙolin kasar Singapore cikin wannan makon.

An sakaya sunayen su saboda tsabar munin laifukan da suka aikata.

A shekarar 2017, mutumin mai shekaru 47, ya amsa gayyatar da abokin aikin sa yayi masa ta zuwa gidan sa domin yin fyaɗe ga matar sa, Channel News Asia ta ruwaito.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe