27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Tsabar kishi: Wani mutum ya halaka masoyiyar sa bayan wani ya ‘dashi’ mazaunan ta

LabaraiTsabar kishi: Wani mutum ya halaka masoyiyar sa bayan wani ya 'dashi' mazaunan ta

Wani mutum mai matukar kishi ya halaka masoyiyar sa bayan wata hatsaniya da suka yi akan zarginta da holewa da kwastoma.

Wata mata mai shekara 50, Ajoke Esomojumi, wacce take sayar da giya a Ikorodu dake jihar Legas ta rasa ran ta bayan masoyin ta, mai suna Victor Dadeowo, ya daba mata wuka yayin wata hayaniya da ta shiga tsakanin su, The Punch ta ruwaito.

City Round ta gano yadda rikicin ya shiga tsakanin mosoyan biyu a yammacin Lahadin da ta gabata a lokacin da suke cikin shagon ta.

An sami labarin yadda Esomojumi da wani kwastoma suke sharholiyar su, yayin da cikin nishadi ya dashi mazaunanta inda Dadeowo ya fassara hakan a rashin kamun-kai.

An tattaro yadda ya nemi Esomojumi da rikici game da holewar, yayin da yayi korafi matuka wanda hakan yasa ta garkame shagonta a cikin wannan daren.

Wakilinmu ya gano yadda Dadeowo yabi Esomojumi har gidan ta dake Church Street, a Ajegunle, yayin da ya cigaba da mita wanda ya kai su har zuwa tsakiyan dare inda ya sharba mata makami a ciki.

jealous lover

Wani mazaunin unguwar wanda ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayyana wa City Round yadda makwabta suka ja kunnen matar game da tashin hankalin da ke shirin aukuwa a lokacin da rikicin ya ta’azzara.


Ya ce, “Matar ba ta da aure, ita kadai take zama. Sun dauki tsawon lokaci suna soyayya da mutumin kuma yana zuwa shagon ta ne.

A wannan ranar ta Lahadi, na gano yadda wani kwastoma yayin wasa da ita a gaban masoyin na ta ya dashi mazaunan ta wanda hakan ne ya fusata shi.

“Ya zargi matar da rashin kamun kai, wanda sanadin haka rikici ya balle tsakanin su. Bayan nan ne suka dawo gidan ta a daren suka cigaba da rigima har mutane suka fahimci musabbabin rikicin.

Lokacin da abubuwa sukayi kamari, makwabta sun ja kunnen ta da ta shiga taitayin ta da mutumin saboda zai iya halaka ta.

“An ji kururuwar ta da misalin karfe 2:00 na daren ranar Litinin, inda wasu mutane suka garzaya don jin abun da ke aukuwa. Amma sai dai lokacin da suka isa gidan nata, sun same ta face-face cikin jini.”

Wata majiya ta bayyana wa wakilin mu yadda Esomojumi ta sheka lahira, inda aka shaida wa dan ta wanda yake zaune a makobta abunda ya ke aukuwa.

An samo labarin yadda aka shaida wa yan sanda a ofishin su dake Owode Onirin, inda suka damko wanda ake zargin.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, CSP Adekunle Ajisebutu, wanda ya tabbatar da kisan, ya ce an maida Dadeowo inda da ake ajiye wadanda suka yi kisan kai na sashin tuhumar sirri da ke Yaba don cigaba da bincike.

Ya ce, “A ranar 31 ga watan Janairu, misalin karfe 2:30 na dare, wata mata ta rasa rayuwar ta sanadiyyar sharba mata wuka da masoyin ta yayi.

Victor Dadeowo ya bi wacce ibtila’in ya fada mata har dakin ta. Al’amarin ya auku ne lokacin da suka samu sabani ita da masoyin nata.

“Yayin bin wani rahoto a ofishin yan sanda dake Owode Onirin, ba tare da bata lokaci ba, masu bincike suka halarci wurin da al’amarin ya auku, inda sukayi nasarar damko wanda ake zargin a maboyar sa.

An adana gawar marigayiyar ne a bangaren adana gawawwakin asibitin anguwar don kammala bincike. Tun lokacin aka mika al’amarin SCIID ga kwamishanan yan sanda, CP Abiodun Alabi.”

Kwaya yake sha yana neman halaka ni, shi yasa na kashe shi – Cewar mahaifiyar da ta kashe dan cikinta

Wata mata ta yiwa kotu bayanin yadda ta kashe dan cikinta, saboda yana shan kwaya, ta bayyanawa kotun cewa ya zame mata alakakai…

Wata mata mahaifiyar yara uku mai shekaru 49, ta amsa laifin ƙitsa yadda za halaka ɗan ta inda ta bayyana cewa shan ƙwayoyi ya ke yi kuma yana takurawa rayuwar ta.

Ziningi Jane Nzama, wacce za ta yi shekaru 20 masu zuwa cikin gidan kaso, ta faɗawa babbar kotun Pietermaritzburg, dake kasar Afrika ta Kudu, cewa ɗan na ta Asanda Kwanda mai shekaru 20 a duniya, ya zama alaƙaƙai a gare ta tun bayan mutuwar mahaifin sa a watan Janairun shekarar 2020.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe