36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Bidiyon wata mata rike da adda tana yi wa diyar ta hargowa ya janyo cece-kuce

LabaraiBidiyon wata mata rike da adda tana yi wa diyar ta hargowa ya janyo cece-kuce

Wata mata ‘yar Najeriya ta yi wa diyarta barazana da adda a wani bidiyo da wani dan Najeriya mai suna Israel Usulor ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Juma’a, 4 ga watan Fabrairun 2022 da misalin karfe 11:24 na dare, inda take gargadin ta da ta kiyayi samari masu damfarar yanar gizo.
Matar ta dauki tsauraran matakai don ganin ta tabbatar diyar ta bata fada hannun’yan damfarar yanar gizo wadanda ake wa lakabi da “Yahoo boys”ba.Matar tayi matukar jan kunnen diyar tata da ta kiyaye kuma kada ta yarda wata alaka ta shiga tsakanin ta da matsafa kuma ‘yan damfarar yanar gizo.

WhatsApp Image 2022 02 05 at 17.18.10
Bidiyon wata mata rike da adda tana yi wa diyar ta hargowa ya janyo cece-kuce


Bidiyon da yayi tashen ya nuna matar rike da zabgegiyar adda a hannun daman ta inda take gargadi, tare da hargowa.
A bidiyon mai ban dariya, anga matar zaune da diyarta a dakin su, inda take tsaye a kanta da zabgegiyar adda.
Yanayin yadda take mata maganar ya janyo cece-kuce daga tarin ‘yan Najeriya a Instagram. Uwar cikin tsananin nuna damuwa take fadi a bidiyon:
“Ina hororki da ki kiyayi ‘yan damfarar yanar gizo.” Diyar ta tambaye ta cikin dariya: “Meyasa kika dauki adda?” Sai mahaifiyar ta amsa da: “Na ce ki zauna a nan ki na kokarin guduwa shiyasa na rike makami.”

Wata mata ta dambara wa mijin ta dutsen guga mai zafi wanda yayi ajalin sa a Legas

Wata mata ta dambara wa mijin ta dutsen guga mai zafi wanda yayi ajalin sa a Jihar Legas.
Matar aure mai suna Motunrayo, ta halaka mijinta mai suna Alaba wanda aka fi sani da Bama, a yankin Abule-Egba a jihar Lagos.

Jaridar PUNCH ta samo bayanai akan cewa ma’auratan sun samu sa’insa ne a tsakanin su wanda daga baya abin ya koma faɗa kaca-kaca.

Ana zargin Motunrayo ta sanya dutsen guga a wuta inda daga bisani tayi amfani dashi wajen ƙona mijinta a ƙirjin sa bayan ya dauki zafi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe