35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Yadda na zama babban biloniya bayan na ajiye kokon almajiranci – Alhaji Isah Gerawa

LabaraiYadda na zama babban biloniya bayan na ajiye kokon almajiranci - Alhaji Isah Gerawa

Wani shahararren attajiri a birnin Kanon dabo ya bayyana yadda ya zama babban biloniya daga almajiranci.

An samu nishadi da raha a wajen ƙaddamar da kamfanin casar shinkafa na Gerawa da gwamnan babban bankin Najeriya Mr Godwin Emefiele yayi a Kano.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban kamfanin casar shinkafar Isah Muhammad Gerawa yayi bayanin sa cikin harshen turanci inda ya bayyana yadda ya taso ga gwamnan babban bankin na Najeriya wanda hakan ya nishaɗantar da mahalarta taron.

image editor output image1145156212 16440557966096292909887592250802
Alhaji Muhammad Isah Gerawa. Hoto daga Facebook

Yadda ya tashi daga almajiranci zuwa biloniya

Ya bayyana yadda ya tashi daga matsayin almajiri a baya ya zama babban biloniya

Mahaifina ya kaini makarantar almajiranci daga ƙauyen mu na Gerawa a shekarar 1965. Na shafe shekaru hudu a makarantar ina koyon ilmin addinin musulunci.”

A lokacin ban faɗawa mahaifina cewa ina son na tsunduma cikin harkokin kasuwan ci ba. A shekara ta hudu na watsar da ƙoƙon bara ta wanda na ke barar neman abinci da shi. Ban gayawa mahaifina ba.

Ya tafi birnin Legas neman arziƙi

Na je ɗaya daga cikin gidajen man da ke hanyar Zaria, inda na haɗu da wani direban babbar mota. Na roƙe shi da ya kai ni jihar Legas, wannan a shekarar 1980 kenan.”

Direban ya amince zai kai ni Legas. Ya siyo min abinci saboda a lokacin ba ni da sisi a waje na. Ya ɗauke ni zuwa Legas. Bayan an sauke ni, na nemi wurin da Hausawa su ke inda aka ce min na tafi Alaba.”

Na tafi zuwa Alaba sai dai bansan kowa ba lokacin a Legas. Na haɗu da wani mutum wanda ya amince na zama ɗan aiken sa, yana sayar da shayi da burodi

Na yi aiki anan a matsayin ɗan aike, inda nake wanke kofuna, kwanuka da kuma ɗebo ruwa. 

Ya sauya sana’a daga baya

Na fahimci cewa na bar Kano ne zuwa Legas domin na samu kuɗi. Amma zama ɗan aiken mai shayi ba zai samar min da wannan kuɗin ba. Saboda haka sai na yanke shawarar canja sana’a. Na fara sayar da kaya da naira ashirin a Alaba zuwa Mile 2 kowace rana har Asabar da Lahadi.” a cewar sa

Lokacin da na dawo arewa, wato nan Kano, na yanke shawarar fara jaraba hannu na akan ƙananan masana’antu inda na fara da sana’ar samar da man gyada

A lokacin na bar gida na da iyalina ina kwana tare da masu gadi saboda tsoron kada a sace injinan wajen da sauran kayayyakin.

Na fara da injina guda biyu waɗanda ake niƙan gyaɗar. Ina cikin masu aiki da injin. Cikin iko da kuma taimakon Allah maɗaukakin sarki mu ka kawo wannan matsayin a yanzu.”

Na samu na kafa wasu kamfanunuwan daga baya, inda a ƙarshe na tsunduma cikin harkar casar shinkafa kamar yadda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar da shawara.”

Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin tono gawar wani Almajiri da ya mutu saboda tsananin azabar da yake sha a wajen Malamin shi

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci a tono gawar wani Almajiri, wanda ake zargin Malamin shi ya kashe shi saboda tsabar azabtarwa.

Dr Muhammad Tahar Adamu, kwamishinan harkokin addini na jihar, shine ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara makarantar dake unguwar Wailari cikin jihar ta Kano, a jiya Talata 1 ga watan Fabrairu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe