24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Babbar Magana: Jam’iyyar APC ta bayyana gwamna a Arewa dake da hannu a ta’addancin dake faruwa a Najeriya

LabaraiBabbar Magana: Jam'iyyar APC ta bayyana gwamna a Arewa dake da hannu a ta'addancin dake faruwa a Najeriya
  • Jam’iyyar APC tayi magana akan matsalar tsaro dake kara cigaba da yaduwa a fadin Najeriya
  • Mai magana da yawun jam’iyyar, Yekini Nabena, ya bayyana mutumin da ya kamata a tuhuma kan wannan hare-hare
  • Dan siyasar kuma yayi kira ga hukumomin tsaro dasu yi duba akan wannan lamari

Babbar jam’iyya mai mulki ta APC ta zargi wani gwamna a yankin Arewa maso Yamma da hannu kan hare-haren ta’addaci da ake kaiwa a yankin.

Kakakin jam’iyyar, Yekini Nabena shine yayi wannan zargi a ranar Alhamis, 17 ga watan Disamba, a Abuja, kamar dai yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yayi zargin cewa rahotannin da aka tara sakamakon bincike ya sanya gwamnan cikin wannan harkalla ta ta’addanci, garkuwa da mutane, da sauran nau’in ayyuka na ta’addanci.

Sai dai kuma, Nabena bai bayyana ainahin sunan gwamnan da yake zargi da wannan aika-aika ba. A cewar jigon jam’iyyar ta APC, ya yanke shawarar boye sunan gwamnan ne saboda wasu dalilai na tsaro.

KU KARANTA: Hotuna: Zahra Buhari da mijinta na murnar cika shekaru 4 da yin aure

Ya ce:

“Hukumomin mu na binciken sirri sun samar da rahotanni da suka alakanta gwamnan na yankin Arewa maso Yamma da hannu wajen daukar nauyin ‘yan ta’adda wajen aikata ta’addanci a wannan yanki.

“Bazan bayyana suna ba saboda wasu dalilai na tsaro. Sai dai kuma ina kira ga hukumomin tsaro da su gabatar da bincike akan wannan magana don tabbatar da sahihancin ta. Bai kamata mu dinga amfani da rayukan al’umma wajen biyan bukatun mu na siyasa ba.”

KU KARANTA: Jerin jihohi 10 a Najeriya da suka fi samun kudaden shiga a shekarar 2020

Jaridar The Tribune, ita ma ta kawo rahoton cewa mai magana da yawun jam’iyyar ta APC, ya zargi babbar jam’iyyar adawa ta PDP akan kokari da take na amfani da wannan matsala ta tsaro wajen biyan bukatun ta.

Har lokacin da muka rubuta wannan rahoto dai jam’iyyar ta PDP bata fito ta kare kanta akan wannan zargi da ake yi mata ba.

Sai dai kuma a wani rahoto makamancin haka, mun kawo muku yadda shugaba Buhari ya zargi manyan Najeriya da hannu wajen sanya Najeriya cikin halin da take ciki a yanzu da kuma halin da za ta shiga nan gaba.

Haka ita ma babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya wato PDP ta bayyana shugaban kasar a matsayin wanda ya kasa tabuka komai a Najeriya a tsawon shekarun da ya shafe yana mulki.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/laabarunhausa/

Twitterhttps://www.twitter.com/labarunhausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: labarunhausaa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe