27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Tirkashi: Bata gari sun sace rawani da sandar Sarki dungurungum

LabaraiTirkashi: Bata gari sun sace rawani da sandar Sarki dungurungum

Wasu ɓata gari mutum biyu, Saheed Olatunji Lukmon, sun shiga hannu a bisa zargin kutsawa cikin faɗar sarkin Iraye, Oba Mosudi Owodina, a ƙaramar hukumar Sagamu ta jihar Ogun.

An samo cewa waɗanda ake zargin, sun ƙutsa cikin fadar ne a ranar 4 ga watan Oktoban 2021, inda su ka sace sandar mulkin basaraken da kuma hadimin sa.

Sai dai an cafke su yayin da su ka dawo ƙauyen domin ƙara tada fitina inda aka samu sandar a hannun su.

PUNCH Metro ta ruwaito cewa, wani mai gadi Temitope Ariyo, mai shekaru 44 ya rasa ransa a hannun ɓata garin da su ka kawo hari a ƙauyen ranar 19 ga watan Janairu.

Ɓata garin da aka cafke
Mutum biyun da ake zargin. Hoto daga Punch

Jaridar ta ruwaito cewa ‘yan bindigan sun auko ƙauyen ne da misalin ƙarfe 3 na rana a bisa umurnin wani mai suna Otunba wanda ya ke iƙirarin cewa kujerar sarautar mallakin sa ce.

Ɓata garin sun kuma rauna ta ‘ƴan sanda uku sannan su ka kwace kayyakin mutane a ƙauyen.

An bayyana abinda ya haifar da rikicin

Oba Owodina, ya bayyana cewa rikicin ya fara ne tun lokacin da aka ɗora shi sarautar garin.

Rikicin ya fara ne bayan an naɗa ni bisa sarautar a 27 ga watan Agusta na shekarar 2016. Ɓata garin sun yi yunƙurin hana naɗa ni. Sai dai ‘yan sanda a lokacin sun hana aukuwar hakan. Duk lokacin da na kawo ziyara garin suna jifa ta da duwatsu da ruwan leda.” a cewar sa

“Na koma Sagamu inda na ke ziyartar Iraye jefi-jefi. Wani mai suna Kalejaiye ya gayyato masu ƙwacen fili daga Ikorodu domin su kawo mana hari. Sun lalata fada ta inda su mayar da ita ɗakin girki inda su ke dafa kaji da awakin sata yayin da mutanen garin su ka tsere.

Ba na iya zuwa garin ba tare da naje ofishin ‘yan sanda na samo masu min rakiya. Akwai makamai a koda yaushe a hannun ɓata garin, sannan sun ƙwace faɗar. Sun lalata fadar da harbin bindiga

Su na yin abubuwa irin na ‘yan ta’adda duk lokacin da su ka shigo garin. A ranar 3 ga watan Satumba, lokacin da na ke son nayi murnar cika shekaru 5 a kan karagar mulki sannan na kafa tubalin ginin ofishin ‘yan sanda, sai da na tabbatar na cewa akwai ‘yan sanda ma su yawa a wurin kafin na samu nasarar taron”

Wata ɗaya bayan taron, sun shigo garin inda suka lalata wurin da zaa yi ofishin ‘yan sandan da dukkanin kayan aikin wajen. Da kyar na tsallake rijiya da baya a hannun su. Wannan ne lokacin da su ka sace sandar mulkin da kuma hadimi na.” a cewar sa

Ƴan sanda daga Abuja sun cafke biyu daga cikin ɓata garin, waɗanda ke ɗauke da sandar da kuma hadimi na, inda su ka tafi da su Abuja domin cigaba da gudanar da bincike. A yadda abubuwa su ke gudana yanzu a Iraye, ba zaa taɓa samun zaman lafiya ba har sai gwamnati ta yi bincike kan rikicin da ke faruwar a garin. Ba na iya jagorantar mutane na cikin kwanciyar hankali.”

Sun buƙaci gwamnati ta kawo musu ɗauki

Shugaban matasan ƙauyen, Ganiu Odugbesan, ya bayyana cewa matasa ma basu tsira ba daga hare-haren da ake kawo wa a ƙauyen.

“Tun lokacin da mu ka samu sabon Oba, ɓata garin sun hana shi gudanar da mulkin sa cikin kwanciyar hankali. Duk lokacin da ‘yan sanda su ka zo yin sasanci, ɓata garin suna korar su, ‘yan sandan suna tsoroɓ faɗa da su. An kore mu daga gidajen mu na gado zuwa wasu sassa na jihar Ogun. ina rokon gwamnatin jihar Ogun da ta kawo mana agaji.

Hukumar ‘yan sanda ba tace komai ba kan lamarin

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, bai amsa kiran da aka yiwa layin wayar sa ba ko dawo da saƙonnin da aka tura masa a lokacin haɗa wannan rahoton.

‘Yan sanda sun cafke wasu matasan da suka kashe budurwar domin yin tsafin kudi da ita

Jami’an ‘yan sanda sun kama wasu matasa uku da laifin kashe wata budurwa domin yin tsafin kudi da ita a jihar Ogun

An kama su ne bayan wani jami’in tsaro ya gansu suna kona wani abu da ake tuhuma wanda ya zama kan mutum a cikin wata tukunya

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye:labarunhausa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe