24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Za mu yi amfani da sihiri da asiri don ganin mun kwato Sunday Igboho daga gidan yari – Agbekoya

LabaraiZa mu yi amfani da sihiri da asiri don ganin mun kwato Sunday Igboho daga gidan yari - Agbekoya
  • Kungiyar manoma ta Agbekoya ta ce ko ta halin yaya sai ta ciro Sunday Igboho daga kurkuku
  • Kungiyar tace tana sane da cewa Jamhuriyar Benin tana tsare da Igboho ne batare da ya aikata laifin da ake tuhumar sa ba
  • A jiya Alhamis ne kungiyar ta yi zanga zange a Osogbo babban birnin Jihar Osun

Kungiyar Agbekoya ta sha alwashi

Kungiyar manoman Agbekoya da ke Najeriya ta sha alwashin cewa sai ta kubutar da dan gwagwarmayar Yarbawa nan, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho daga gidan yarin jamhuriyar Benin.

Yayin da suke gudanar da zanga-zanga a Osogbo babban birnin jihar Osun a ranar Alhamis 3 ga watan Fabrairu, kungiyar ta ce za su yi amfani da karfinsu na asiri wajen ganin sun kubutar da Igboho.

Dan gwagwarmaya Igboho badan ta’adda ba ne

Da yake magana a madadin kungiyar, shugaban kungiyar Cif Kamorudeen Okikiola, ya jaddada cewa fa Igboho ba dan ta’adda ba ne dan gwagwarmaya ne.

Sunday Igboho
Za mu yi amfani da sihiri da asiri don ganin mun kwato Sunday Igboho daga gidan yari – Agbekoya

Yace:

“Sunday Igboho ba dan ta’adda ba ne mun san cewa an tsare shi ne ba bisa ka’ida ba, gwamnatin Jamhuriyar Benin ta dai na zaman kotu da shi. Don haka muna neman a sake shi ta hanyar da ta da ce. Idan kuma sun ƙi, za mu yi amfani da duk wani karfi da muke da shi na sihiri don ganin mun fitar da shi daga kurkuku.

Mu na nan muna shiri

Ina sake jadadawa, mu al’umar Agbekoya, za mu fitar da shi daga gidan kaso na Jamhuriyar Benin, mu dawo da shi gida, “in ji shi

Ya yi tir da yadda ake ta fama da matsalar rashin tsaro a fadin kasar, yana kuma kara jan kunnen yanda ‘yan siyasa ke yin biris da damuwan talakwa.

Masu zanga-zangar sun taru ne a Olaitan daga nan suka wuce ta Odi-Olowo, Asubiaro, Isale-Osun, Idi-Omo zuwa Ataoja inda nan ne fadar Osobo Oba Jimoh Olaonipekun yake inda suka mika wa sarkin masarautar wasika kan bukatar su da suke so wanda wasikar ta fito ne daga hannun shugaban su.

Malami da Buratai ne suka sa aka tsare Sunday Igboho a Cotonou – Kungiyar Yarabawa

Masu yunkurin kafa kasar Yarabawa, sun zargi Ministan Shari’a Abubakar Malami; da kuma tsohon hafsan hukumar soji ta Najeriya, kuma jakadan Najeriya a jamhuriyar Benin, Tukur Buratai, da hannu kan tsare Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho a Cotonou.

A ranar Litinin ne dai aka aika Sunday Igboho, shugaban masu rajin kafa kasar Yarbawa, gidan yari, inda ake zargin sa da wasu sabbin tuhume-tuhume.

Haka kuma wata kungiyar Yarbawa ta kai da kai ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari, da sauran jami’an gwamnatin Najeriya da su daina zaluntar dan Adam ko kuma su fuskanci mummunan sakamako.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan kungiyar, Oluwafemi Oluwajuyitan, sun bukaci shugaba Buhari da sauran shugabannin Najeriya da suke matsa lamba a Jamhuriyar Benin akan a daure Igboho, cewar su tuna babu wani da yake dauwama.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe