24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Matashiyar ɗaliba ta karya tarihin shekara 60 a ABU Zaria, ta kammala da sakamakon da ba a taɓa samu ba

LabaraiMatashiyar ɗaliba ta karya tarihin shekara 60 a ABU Zaria, ta kammala da sakamakon da ba a taɓa samu ba

Wata ‘yar Najeriya ta ba mutane mamaki da kwazon da ta nuna a jami’ar Ahmadu Bello University, Zaria

Zainab Bello ta zama mace ta farko da ta kammala karatun ta da daraja ta ɗaya (first class) a sashen Mathematics inda ta karya wani dadadden tarihi mai shekaru 60

Haziƙar matashiyar dai ta daɗe tana nuna ƙwazo tun tana ‘yar ƙaramar yarinya

Tun lokacin da aka kafa jami’ar Ahmadu Bello University, Zaria a shekarar 1962, ba wata ɗaliba mace da ta taɓa gamawa da daraja ta ɗaya (first class) a sashen Mathematics.

An kafa sabon tarihi

Sai dai yanzu wata hazikar matashiya mai suna Zainab Bello ta karya wannan tarihi. Zainab ta kammala da CGPA 4.85, abinda baa taɓa samu ba.

An dai kafa Sashen na Mathematics tun a shekarar 1962 lokacin da aka buɗe jami’ar ta ABU.

Tun tana ƙarama ta ke nuna hazaƙa

Ƙwazon da Zainab ke nuna wa ba yanzu kawai ya fara ba. A wata wallafa da Mohammed Ali yayi a shafin Facebook, ya nuna cewa tun Zainab na ƴar ƙarama ta ke zama ta ɗaya a kowane aji.
Ga abinda wallafar ke cewa:

Wannan ita ce Zainab Bello, ɗalibar da ta samu sakamako mafi daraja wato 1st class da CGPA 4.85 a sashen Mathematics, inda ta zama mace ta farko wacce ta gama da wannan sakamakon. Tun ta na ƴar ƙarama ta ke kasancewa ta ɗaya a dukkanin makarantun da taje sannan kuma ta haddace Al-qur’ani mai girma tun ta na ƴar shekara 11.  Ina ta ya ki murna, Allah ya sanya wa sakamakon ki albarka”

‘Yan Najeriya da yawa sun taya ta murna

Ƴan Najeriya da dama da su ka ga hazaƙar da Zainab ta nuna, sun taya ta murna sosai. Ga ƙadan daga cikin waɗanda su ka bayyana ra’ayin su:

Felix Okwudili Anibisi ya rubuta:

“Na ta ya ki murna, fatan samun nasara”

Garba Isa ya rubuta:

Ina mi ki fatan nasara a matakin da za ki taka na gaba.”

Na’Annabi Sagir Muazu ya rubuta:

Ina ta ya wannan matashiyar murna. Ta cancanci yabo, ƙarfafa guiwa, kyaututtuka da kuma addu’oi”

Matashi da ya samu A takwas a WAEC, ya kammala digiri da sakamako mai daraja ta ɗaya a jami’a

Wani matashi ya nuna sakamakon jarabawar WAEC da jami’a bayan ya kammala karatun digiri ɗinsa na farko a fannin injiniyanci

‘Yan Najeriya da dama da suka shiga shafinsa na Twitter sun yaba da kokarinsa yayin da wasu ke ba shi shawarar da ya yi aiki don samun kwarewa ta fannin kasuwanci ganin cewa ya kammala karatunsa da 4.86 CGPA, wata kungiya mai zaman kanta a Amurka ta yi masa magana idan ya na son tallafin karatu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe