34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ku tona asirin barayin kasa mu kuma mu biya ku, Bawan EFCC ya yiwa matasan Najeriya sabon albishir

LabaraiKu tona asirin barayin kasa mu kuma mu biya ku, Bawan EFCC ya yiwa matasan Najeriya sabon albishir

Bawa ya bukaci mutane suyi amfani da sabuwar manhajar tonon asiri da EFCC ta kaddamar mai suna “Eagle Eye”, wajen tona asirin masu ta’annati da dukiyar kasa…

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce ‘yan Najeriya suna da ikon samun kudi idan suka tona asirin masu satar dukiyar kasa, idan har aka samu damar kwato dukiyar da suka sata.

Bawa ya bukaci al’umma su rungumi tsarin ba da bayanan sirri

A rahoton da jaridar Pulse ta ruwaito, shugaban na EFCC ya bukaci matasa da sauran jama’a da su rungumi tsarin ba da bayanan sirri na hukumar domin samun kudaden shiga ta wannan hanya.

Bawa ya yi wannan roko ne a ranar Laraba, 2 ga watan Fabrairu, 2022, a lokacin da wasu masu fada a ji a shafukan sada zumunta a karkashin kungiyar Mofeto Miracle Church a Abuja.

Bawan EFCC ya yiwa matasan Najeriya sabon albishir
Bawan EFCC ya yiwa matasan Najeriya sabon albishir

Hukumar ta wallafa sanarwar a shafinta na Facebook

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin Facebook, Bawa ya ce har yanzu manufar tana aiki.

Bawa ya kuma kara karfafawa mutane guiwa da su yi amfani da manhajar rahoton EFCC, Eagle Eye, wajen kai rahoton laifukan masu yiwa tattalin arziki zagon kasa.

A nata jawabin, kungiyar karkashin jagorancin marubuci kuma dan rajin kare hakkin bil’adama, Richard Akinola, ta ce sun bi diddigin ayyukan hukumar EFCC karkashin jagorancin Bawa, kuma sun fahimci cewa akwai bukatar hada karfi da karfe wajen yaki da cin hanci da rashawa.

An kaddamar da wannan manufa ta tona asirin masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a farkon mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wani bangare na kokarin da take na yaki da cin hanci da rashawa.

EFCC ta cafke Sanata mai ci da matarsa kan zargin almundahana da kudin al’umma

Jaridar Premium Times ta ruwaito zargin kama tsohon gwamnan jihar Nasarawa, kuma Sanata mai ci, Tanko Al-Makura da matarsa Mairo, da hukumar EFCC.

Ba tare da ta bayyana majiyar rahoton ba, jaridar Premium Times ta kara da cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta gurfanar da ma’auratan a babbar helkwata dinsu da ke babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai jaridar ta kara da cewa ba a tabbatar da zargin da ake yiwa gwamnan da matarsa ba.

Amma, wasu majiyoyin sun bayyana cewa kama sun na da nasaba da zargin almundahana da kuma almubazzaranci da gwamnan yayi da kudin al’umma a lokacin da yake kan mulki.

A na ta rahoton Jaridar Daily Trust, wacce ta boye majiyar ta, ta bayyana cewa Al-Makura da matarsa sun kai kansu ofishin EFCC ne ba wai kama su aka yi ba.

Ta kara da cewa daya daga cikin majiyarta ta nuna cewa hukumar ta kama ma’auratan ne bayan sun kasa bada cikakken bayani a kan almubazzaranci da dukiyan al’umma da suka yi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe