24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Dattijo ya shirya jana’izarsa, ya sayi kayan ciye-ciye da baƙi za su ci lokacin makokinsa

LabaraiDattijo ya shirya jana'izarsa, ya sayi kayan ciye-ciye da baƙi za su ci lokacin makokinsa

Wani dattijo mai shekaru 70 mai suna Leo, wanda watakila ya ga abin da zai faru a nan gaba ya shirya duk abin da za a buƙata a lokacin jana’izarsa. Leo ya bayyana cewa dole ne ya yi hakan domin tsofaffin da ke mutuwa a ƙauyensa sun zama nauyi mai yawa na kuɗi ga mazauna ƙauyen.

Haka kuma, ya na da mata tara ta siyo abin sha, akwatin gawa, da duk wani abu na bikin binnewa

Dattijo
Dattijo ya shirya jana’izarsa, ya sayi kayan ciye-ciye da baƙi za su ci lokacin makokinsa

Dattijo ya sanar da dalilin daukar wannan mataki

Wani dattijo mai shekaru 70, Leo, ya tona kabarinsa a shirye-shiryen mutuwarsa. Dattijon ya ce ya dauki matakin ne domin talakawan al’ummar sa sun sha wahala wajen binne mutanen da suka mutu kwanan nan.

A cikin wani shirin bidiyo na Afrimax, mutumin ya bayyana cewa ba ya so ya zama nauyi ga mutane bayan ya tafi. Dattijon ba ya son ya zama nauyi ga wasu.

An biya komai don cimma wannan manufa, Dattijon ba kawai ya tona kabarinsa ba, ya shirya duk abin da za a yi amfani da shi yayin jana’izarsa.

Dattijon ya sayi isassun abubuwan sha don nishadantar da baƙi da za su yaba da taron. Ya kuma samu siminti da bulo na kabari.

Dattijo Leo wanda ke da mata tara ya biya wa masu ɗaukar nauyinsa a gaba. Tun lokacin da aka yi jana’izar sa, Dattijon ya yi amfani da lokacinsa don yin bikin sauran kwanakin da ya yi a duniya.

A lokacin rubuta wannan rahoto, bidiyon ya haifar da sharhi kala-kala

Ga wasu daga cikin martanin:


franca_onome ya ce: “Shi mutum ne mai hikima. A Afirka ne kawai za mu bar nauyin jana’izar mu ga ‘yan uwan ​​da suka rigaya suna cikin makoki. ‘Yan Afirka ba sa shirin mutuwar su. Suna so su tafi aljanna amma ba su son mutuwa, Mutuwa bashi ce, dole ne mu biya duka don haka me zai hana mu saukaka wa masoyan mu ta hanyar ceton su daga cin bashi a kan kudaden jana’izar mu? Shirya kashe kuɗin ƙarshe ta hanyar kamfanin inshora mai kyau ko kuma ku yi shi da kan ku. .”

kingmac_47 ya ce: “Dattijo mai hangen nesa.”

Hadi Usman dattijo mai shekaru 67 da ya kirkiro murhu mai amfani da ruwa da baya bukatar gas ko kalanzir

Wani hazikin dattijo dan Najeriya da ke zaune a unguwar Jeka da fari da ke jihar Gombe ya kawowa jama’a sauki inda ya yi kokarin kirkirar sabon samfurin murhun dafa abinci, wanda ya ke amfani da ruwa, Hadi Usman mai shekara 67 da haihuwa, ya kirkiri murhun girki wanda baya bukatar amfani da gas ko kalanzir wajen kunna shi.

Dalilin da yasa ya kirkiri wanan murhu mai aiki da ruwa

Kamfanin dillancin labarai na PR Nigeria ya ruwaito cewa, dattijon wanda yake makeri ne ya kirkiro wanan fasaha ne saboda burinsa na son bayar da tallafin wajen ganin an samu saukin rayuwa.

Wani faifan bidiyo na YouTube wanda kafafen yada labarai suka yada ya nuna yanda Malam Hadi Usman yake bayani kan yadda ake amfani da murhun.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe