34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Budurwa ta shiga tashin hankali, bayan ta gano saurayin da suka shafe shekara 5 suna soyayya ya shekara 7 da igiyar aure a kanshi ba ta sani ba

LabaraiBudurwa ta shiga tashin hankali, bayan ta gano saurayin da suka shafe shekara 5 suna soyayya ya shekara 7 da igiyar aure a kanshi ba ta sani ba

Wata budurwa mai amfani da kafar sadarwa ta Twitter ta hau shafinta ta bayyana halin da kawarta ta shiga bayan ta gano cewa saurayinta da suka shafe shekara biyar suna soyayya ya shekaraa bakwai da igiyar aure a kanshi ba tare da ta sani ba.

A cewar budurwar mai suna @Chrisssssy_Payn a shafinta na Twitter, kawarta ta gano cewa saurayinta yana da aure, bayan ya wallafa hotunan matarshi a WhatsApp yana su murnar cika shekara bakwai da yin aure.

Ya yiwa matarshi kayar daga ita ba wata

@Chrisssssy_Payn ta ce mutumin yayi ta koda matarshi a WhatsApp har yana gaya mata cewa ita kadai ce mace daya da yake so a rayuwar shi.

Da take bayyana yadda lamarin ya kasance a shafinta na Twitter, ta ce:

“Yanzu kawata ta gano cewa saurayinta da suka shafe shekara biyar suna soyayya ya shekara bakwai da aure a kanshi, bayan ya wallafa hotuna yana murnar cikar su shekara bakwai da aure. Ya wallafa hotunan a shafinsa na WhatsApp yana nuna irin soyayyar da yake nunawa matarshi, har yana cewa ita kadai ce mace a rayuwar shi.”

Budurwa

Sharhin mutane kan wannan rubutu

Ga sharhi da mutane suka dinga yi a kasan wannan rubutu na ta:

“Daga yaya za ki shafe shekara biyar cur kina soyayya da mutum ba tare da sanin cewa yana da aure ba? Gaskiya wannan babu kamshin gaskiya a ciki, kiyi hakuri.”

@_fauzeey

“Ba ta ga wata alama ba kwata-kwata? Shin basa yin magana da dare ne? Magana da dare zai taimaka sosai.”

@fashion_magicblog

“Wannan abu ya zama ruwan dare ai, ya taba saurayin kawarki, kema ki saurari naki yana nan zuwa.”

@capry_sunn

An daura auren saurayi da budurwa da suka hadu a shafin Twitter

Wani ango mai suna Aminu da amaryarsa mai suna Yetunde, sun sanar da duniya yadda Allah ya hada su har soyayyar da suke ta kai su ga yin aure.

A wani hoto da Aminu ya wallafa a shafin sadarwa, ya nuna yadda soyayyar su ta fara, inda ya aikawa Yetunde sakon farko a shafin Twitter a shekarar 2018.

A cikin hirar ta su ta farko, Aminu ya gabatar da kansa bayan tambayar yadda take.

A cewar Aminu ya dauki lokaci mai tsawo yana bibiyar Yetunde da kuma yadda take wallafa rubutun ta a shafinta na Twitter kafin daga baya ya yanke shawarar yi mata magana.

Kada ku yi tsautsayin auren namiji da yake wanka sau 3 a rana – Budurwa ta shawarci ‘yan mata

Wata kyakyawar budurwa mai ban dariya ta bawa ‘yan mata shawarar da ta jawo akayi ta tafka muhawara a kafofin sadarwa na zamani.

A wani rubutu da ta wallafa a shafin ta na twitter, ta baiwa ‘yan mata shawarar da suyi watsi da maganar auren duk wani namiji mai wanka sau uku a rana.

Sai dai kuma wani abin mamaki, shine, jami’ar Harvard ta fannin likitanci dake kasar Amurka ta taba wallafa wani rubutu wanda yake kama da abinda budurwar ta, hakan ya sanya wasu ke ganin abinda budurwar ta fada gaskiya ne.

Budurwar ‘yar asalin kasar Ghana dake zaune a Najeriya ta jawo kace nace a kafar sadarwa ta Twitter, bayan ta samu da dama sun ba ta goyon baya kan wannan magana da tayi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe