34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Abokai 3 da aka haifa shekara daya, suka yi makaranta daya, suke zaune a gida daya, sun mutu an binne su a waje daya

LabaraiAbokai 3 da aka haifa shekara daya, suka yi makaranta daya, suke zaune a gida daya, sun mutu an binne su a waje daya
  • Aminan juna ‘yan shekaru 22 sun rasa ransu sanadiyan hatsarin mota
  • Abokan sun kasance tamkar ‘yan gidan daya komai na su a tare suke yi
  • An yi jana’izan su da misalin karfe 2 na ranar juma’a

Abokan su uku, ‘yan shekara 22 sun kasance kansu daya, inda suke gudanar da rayuwarsu a Al-Khobar, sun rasa rayukansu ne a wani hatsarin mota da ya rutsa da su. Sun kasance ‘yan asalin garin Damam ne.

  • Shafeeq:  Ya fito daga gundumar Malappuram ya kammala karatunsa wanda kafin mutuwarsa yana aiki ne tare da mahaifinsa mai suna Saidalavi Haji a wata cibiyar kasuwanci.
  • Ansif: Ya fito daga gundumar Wayanad, yana gaf da kammala karatunsa a Bahrain.
  • Sanad: Kuwa ya fito daga gundumar Kozhikode yana fafutukar komawa makaranta domin samun ilmi mai zurfi inda yake jiran a ɗage takunkumin tafiye-tafiye da aka kakaba saboda barkewar cutar Covid-19.

Makarantar su daya, ajin su daya, makwancin su na kabari ma daya

Sun yi karatunsu tare a International Indian School of Damam. Sun taso tare tun kuruciya har samartakar su tare ga shi kuma yanzu kabarurukansa manne da na juna.

Rahotanni sun bayyana cewa motar tasu ce ta rasa birki a hanyar da ke kan titin Damam Al Khobar wanda ke kusa da Dhahran. Inda Motar ta su ta bugi wasu motoci, ta dinga juyi akan titi sannan daga bisani ta kife, wanda hakan ne ya yi sanadiyar mutuwar su.

Jana’iza

Ma’aikatan jin dadin jama’a na Nas Vakkam, Jaafar Kondotty, da Shaji Wayanad, su suka dauki nauyin binne su. Mutane da dama Sun halarci Damam Medical Complex inda aka ajiye gawarwakin da kuma wurin sallar jana’izar su wanda akayi a Asibitin Damam da misalin karfe biyu na ranar Juma’a.

Kwaya yake sha yana neman halaka ni, shi yasa na kashe shi – Cewar mahaifiyar da ta kashe dan cikinta

Wata mata mahaifiyar yara uku mai shekaru 49, ta amsa laifin ƙitsa yadda za halaka ɗan ta inda ta bayyana cewa shan ƙwayoyi ya ke yi kuma yana takurawa rayuwar ta.

Ziningi Jane Nzama, wacce za ta yi shekaru 20 masu zuwa cikin gidan kaso, ta faɗawa babbar kotun Pietermaritzburg, dake kasar Afrika ta Kudu, cewa ɗan na ta Asanda Kwanda mai shekaru 20 a duniya, ya zama alaƙaƙai a gare ta tun bayan mutuwar mahaifin sa a watan Janairun shekarar 2020.

Ta bayyana cewa ɗan ta ya fara shan ƙwayoyi sannan yana ɗaukar motocin gidan ba tare da izni ba.

Nzama, wacce ta cigaba da gudanar da sana’ar taxi ɗin mijinta, ta faɗa cewa yaron nata zai lalata motocin sannan ya jira sai ta biya kuɗin gyara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe