27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Kamfanin kera motoci da Dangote ya bude a Kaduna ya fara aiki, inda za a dinga kera motoci 120 a kowacce rana

LabaraiKamfanin kera motoci da Dangote ya bude a Kaduna ya fara aiki, inda za a dinga kera motoci 120 a kowacce rana
  • Dangote ya hada hannu da wasu masu hannu da shuni sun kaddamar da kamfanin hada motoci kira peugoet a Gida Najeriya
  • Manajan kamfanin yace burin su shine su ga kamfanin ta daukaku har zuwa kasashen ketare
  • Kamfanin zai dinga samar da motoci 120 a kulum da ga lokacin da aka fara aiki

Kamfanin Dangote zai kera motoci

Kamfanin motocin Dangote kirar Peugeot Automobiles Nigeria (DPAN), ko da dai an samu bayanin cewa ba wai duka kamfanin ba ne mallakin sa wani bangare ne na shi, wani bangare kuma na gwamnatin jihar Kebbi da kuma Stellantis Group, kamfanin ya fara aikin hada motoci kirar Peugeot a nan gida Najeriya. An kaddamar da shi ne a shekarar 2018 wanda ya ke a garin Kadunar Najeriya.

A yadda rahotanni suka nuna, ana sa ran akalla kamfanin zai dinga samar da motoci kimanin 120 a kowacce rana. Ana hasashe cewa hada motocin zai iya kai wa daga yanzu zuwa shekarar 2023 wanda za a yi su isassu don ganin sun shiga lungu da sako na kasuwannin gida Najeriya da kuma nahiyar Afirka baki daya.

Dangote
Kamfanin kera motoci da Dangote ya bude a Kaduna ya fara aiki, inda za a dinga hada motoci 120 a kowacce rana

Nau’ikan motocin da ake sa ran za a kera

Nau’ikan motocin da ake sa ran kamfanin zai kera sun hada da Landtrek, 3008, 5008 da kuma 508. Yayin da aikin ya fara, ana sa ran za a faɗaɗa kirkiran wasu nau’ikan motoci don ganin an cimma bukatar kasuwar motoci a Najeriya.

Kamfanin zai kera motoci na kere sa’a

Domin samar da samfarin motoci irin kiran sauran ƙasashen duniya, za a tabbatar da an kure fasaha wajen kiran wannan motoci, da kuma nau’ikan samfuri daban daban sannan ga aminci wanda hakan ne zai sa su fita zakka da sauran motoci domin jan ra’ayin jama’a da abokan ciniki.

Bayanin manajan kamfanin game da yadda kirar motocin za su kasance

An ruwaito cewa manajan daraktan kamfanin motocin dangote, Ibrahim Issa Gachi ya bayyana cewa;

“Da New Green Field Ultima Assembly Plant, DPAN ta yi abubuwa da dama don ganin kamfanin Peugeot ya samar da kayayyakin gyara da kuma samar da isasun motocin kamfanin ga ‘yan Najeriya.

Abokan aikinmu na fasaha su za su kara ƙarfafawa DPAN gwiwa don ganin an kera motoci ba tare da sun dau lokaci mai tsawo ba don gamsuwar abokan ciniki mai dorewa.”

Ya ci gaba da cewa;

“Wannan mafarkin ya fara ne a lokacin da aka kaddamar da kamfanin Peugeot a Najeriya da kuma taron hada motoci kirar 301 da ya gudana a nan cikin gida Najeriya, wanda ya gudana a sabuwar masana’antar mu ta Kaduna, daga nan kuma aka fara amfani da Landtrek, 3008, 5008 da sabuwar 508.

Babu wani abu da aka keɓe wai don a sake kaishi kasuwa da ga baya. don haka muka hada hannu don ganin an kai ga cin nasarar habaka kasuwar wannan kamfani, inda mu ke da burin kera motoci sama da 100,000 a kowace shekara”

Pan Nigeria Peugeot
Kamfanin kera motoci da Dangote ya bude a Kaduna ya fara aiki, inda za a dinga hada motoci 120 a kowacce rana

Ya kara da cewa;

“Babu wani abu da aka kebe domin kwadayin siyan hannun jari a kasuwa, shi yasa muka hada hannayen mu don tabbatar da ci gaba mai dorewa a kasuwar da ke da burin kera sama da motoci 100,000 a kowace shekara,” in ji shi.

Dangote ya shafe shekaru 11 a jere yana zama bakar fata na 1 da yafi kowa arziki a nahiyar Afirka da kuma duniya baki daya

Mujallar Forbes ta fitar da jerin sunayen hamshakan attajirai wanda ta ke yi kowacce shekara a inda ‘yan Najeriya uku kacal ne kacal suka samu wannan nasarar, Aliko Dangote, Mike Adenuga da kuma Abdul Samad Rabiu.

Ta bayyana hakan ne a cikin wani sako da ta fitar a yanar gizo a ranar Litinin, inda ta bayyana jerin sunayen attajiran da suka fi kowa kudi a nahiyar Afirka a shekarar 2022, sunan mutum daya ne kawai ba tayi nasarar samun wannan kambu ba a wannan shekarar, ita ce Folorunsho Alakija.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye:labarunhausa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe