24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Mutane na ta sanyawa Ali Nuhu albarka kan yadda ya yiwa wata mai tallar awara goma ta arziki lokacin da ta yi bari

LabaraiKannywoodMutane na ta sanyawa Ali Nuhu albarka kan yadda ya yiwa wata mai tallar awara goma ta arziki lokacin da ta yi bari

Mutane na ta sanyawa jarumi Ali Nuhu albarka, kan yadda ya tallafawa wata yarinya mai tallar awara goma ta arziki, bayan ta yi barin awara…

Duk da irin suka da kahon zuka da akan kafa akan jaruman masana’antar Kannywood wani lokacin sukan yi abin da wasu daga cikin al’umma ke yaba musu gami jinjina musu da fatan su zama abin koyi ta wannan fanni.

Wadanda suka fi samun wannan yabo sun hada da Hadiza Gabon, Mansurah Isah, Ali Nuhu, Adam A Zango, Aisha Humaira da dai sauran su.

A wannan karon jarumi Ali Nuhu ne yayi wani abin arziki, inda abokin sana’arsa, Abdul Saheer, wanda aka fi sani da Malam Ali a cikin shirin “Kwna Casa’in” ya wallafa a shafinsa cewa wani abokinsa ya bashi labarin abin kirkin da yayi akan idon sa, inda ya rubuta cewa:

Ali Nuhu

Rubutun da Malam Ali ya wallafa a shafin shi

“Jiya nake hira da wani abokina, sai yake ce min Abdul Wallahi Ali Nuhu ya taba yin wani abu wanda ya taba ni, nake tambayarshi, mene ya faru?

Sai ya ce watarana ya ga wata yarinya mai tallar Awara tana kuka alamar tayi barin awarar ta. Sai ga Ali Nuhu ya fito yana zuwa ya ga yarinyar tana ta sharbar kuka, nan take yaje har inda yarinyar take ya tsaya yake tambayarta shin mene yake faruwa dake?

Sai ta ce awarar ta ce ta bare, sai ya ce to daina kuka kinji, ya dauri kudi masu kauri ya ce ga wannan rike na baki duka kije, amma fa ki daina kuka.

Bayan Ali Nuhu ya shiga mota ya tafi sai mutanan wajen suka ce wannan kudin da ya bawa wannan yarinyar fa yanzu yayi wani aikin “Voice Over” aka bashi kudin, ko aljihu bai saka kudin ba ya dauka ya bawa wannan yarinyar.

Abokina ya ce shifa tun daga nan ya sallamawa Ali Nuhu akan gaskiya wannan mutumin kirki ne.

Muna alfahari da kai matuka sir

Screenshot 2022 02 03 170709

Ali Nuhu ya yi sharhi a kasan rubutun

Bayan wallafa wannan rubutu, mutane da dama sunyi ta tofa albarkacin bakin su, inda hadda shi jarumi Ali Nuhu ya ce wani abu, inda yayi sharhi da cewa:

“Na gode, Allah ya sa mu dace gaba daya.

Na dauki nauyin kula da marayu har na aurar da daya ba tare da kowa ya sani ba – Bello M Bello

A wata hira da kafar yada labarai ta DW Hausa tayi da jarumi Bello Mohammed Bello, ya bayyana cewa gwamnati ko wata kungiya ba ta biyan sa aikin wayar da kan matasa da yake yi.

Ya ce yana yin haka ne kawai domin sauke hakkin mutuntaka, inda a cikin hirar ya bayyana cewa har marayu ya raina guda uku suka girma a gaban shi har ya aurar da daya.

Ya ce marayun yana rike da su tun lokacin rikicin addinin da aka yi da Jos a shekarar dubu biyu da daya (2001), inda aka samu asarar rayuka da dama a lokacin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe