24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Kwaya yake sha yana neman halaka ni, shi yasa na kashe shi – Cewar mahaifiyar da ta kashe dan cikinta

LabaraiKwaya yake sha yana neman halaka ni, shi yasa na kashe shi - Cewar mahaifiyar da ta kashe dan cikinta

Wata mata ta yiwa kotu bayanin yadda ta kashe dan cikinta, saboda yana shan kwaya, ta bayyanawa kotun cewa ya zame mata alakakai…

Wata mata mahaifiyar yara uku mai shekaru 49, ta amsa laifin ƙitsa yadda za halaka ɗan ta inda ta bayyana cewa shan ƙwayoyi ya ke yi kuma yana takurawa rayuwar ta.

Ziningi Jane Nzama, wacce za ta yi shekaru 20 masu zuwa cikin gidan kaso, ta faɗawa babbar kotun Pietermaritzburg, dake kasar Afrika ta Kudu, cewa ɗan na ta Asanda Kwanda mai shekaru 20 a duniya, ya zama alaƙaƙai a gare ta tun bayan mutuwar mahaifin sa a watan Janairun shekarar 2020.

uwa ta kashe danta mai shan kwaya
Ziningi Jane Nzama a kotun da ake shariar danta da ta kashe mai shan kwaya. Hoto daga Naijanews

Matar ta bayyana dalilin halaka yaron

Ta bayyana cewa ɗan ta ya fara shan ƙwayoyi sannan yana ɗaukar motocin gidan ba tare da izni ba.

Nzama, wacce ta cigaba da gudanar da sana’ar taxi ɗin mijinta, ta faɗa cewa yaron nata zai lalata motocin sannan ya jira sai ta biya kuɗin gyara.

Yana min tsawa sannan ya ci min mutunci a kullum” a cewar ta

Ta kuma ƙara bayyana cewa yaron na ta yana sace makullan motocin sannan ya ɗauki abokan sa su je shan ƙwaya ba tare da izni ba. Ta ƙara da cewa duk lokacin da ta tsawatar masa sai ya ce mata kasuwancin gadon shi ne sannan ba ƙarƙashin ikon ta ya ke ba.

Ta nemi taimakon saurayin ta wajen halaƙa ɗan na ta

A watan Fabrairun 2021, Nzama ta fara soyayya da Mthokoziseni Majozi inda ta bayyana masa tana son ya taimaka mata wajen halaka ɗan ta. Shi kuma ya amince da hakan.

A watan Maris, sun bayyana wa wani mutum Simphiwe Silangwe, shirin su. Silangwe shine zai zama yaron Nzama lokacin da za su yi wa mamacin tsarin inshorar rayuwa ta wayar tarho.

Bayanan kotu sun nuna cewa mutanen uku suna haɗuwa lokaci bayan lokaci inda su ka yanke cewa zaa harbi mamacin ne a lokacin da ya ke cikin gida.

A safiyar 14 ga watan Aprilu, Nzama ta bayyana cewa Majozi ya kira ta a waya inda ya ce mata ta duba ɗan ta.

Ta bayyana cewa lokacin da ta shiga daƙin sa, ta tarar da ya mutu, sannan ta fara ihun sanar da makwabtan ta. Daga baya an kira ‘yan sanda.

Watanni ƙadan bayan aukuwar lamarin,  Nzama, wacce ta ke da wasu yaran guda biyu, yarinya ‘yar shekara 12 da yaro ɗan shekara 16, ta shiga hannun hukuma inda ta amsa laifin ta ba tare da ɓata lokaci ba. Ta amsa cewa tana sane ta aikata laifin da sauran mutum biyun da ake tuhuma.

Wata mata ta sha dakyar bayan dan da ta haifa yayi kokarin kashe ta da wuka

Wata mata ta kusa rasa ranta bayan dan da ta haifa ya kai mata hari da wuka yana shirin kashe ta.

Matashin saurayin dan asalin jihar Imo ya shiga hannun ‘yan sandan jihar, kan zargin shi da ake na cakawa mahaifiyarshi wuka a wurare daban-daban a mahaifar shi Owerri, a safiyar ranar Litinin 24 ga watan Janairu

Wani da lamarin ya faru akan idon shi ya bayyana cewa saurayin ya kira mahaifiyar shi, inda yayi amfani da wannan dama ya dinga caka mata wuka

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe