29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Sojan da dan sanda ya kashe a fadar Shehun Borno shine ya kare Shehun Borno daga harin bam da aka kai masa

LabaraiSojan da dan sanda ya kashe a fadar Shehun Borno shine ya kare Shehun Borno daga harin bam da aka kai masa

Sojan da aka halaka a fadar Shehun Borno, Donatus Vonkong, cikakken jarumi ne wanda ya kusa yin mutuwar jarumta a baya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wani ɗan sanda cikin yanayin maye ya halaka Vonkong har lahira.

An bayyana yadda sojan ya rasa ran sa

Wata majiya ta bayyana cewa mamacin jajirtaccen jarumi ne wanda ya kare Shehun Borno daga harin ƙunar baƙin wake a shekarar 2012.

MOPOL ɗin sun dawo daga  Sintiri amma yana cikin mayen giya. Da farko, sojan ya so ya amshe bindigar sa amma sai ya ƙyale shi. Bayan wasu ‘yan mintuna kawai sai ya fara harbi kan mai uwa da wabi inda cikin tsautsayi ya harbi sojan a kumatu, nan take ya mutu.

An kashe soja a fadar Shehun Borno

“Sanannen abu ne cewa Donatus Vonkong jajirtaccen soja ne. A shekarar 2012, ya kare Shehun Borno daga harin bam na ƙunar bakin wake. Ya rike mai ɗauke da bam ɗin sannan yayi waje da shi. Bam ɗin ya fashe inda yaji masa rauni a ƙafa. Mutum ne wanda mutane ke matuƙar son sa” a cewar wata majiyar

An naɗa sojan sarauta a fadar Shehun Borno

A shekarar 2019, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi, ya ba Donatus sarauta a fadar sa.

Shehun na Borno ya naɗa Vonkong a matsayin ‘Zanna’, wanda ke nufin dogari.

Ko kana cikin aiki ko ka aje aiki, an baka damar yin ayyukan ka a matsayin ka na Zanna a wannan fadar.” Shehun Borno ya faɗa bayan naɗin Vonkong.

Haka kuma, Shehun na Borno yayin adduar samun zaman lafiya mai ɗorewa a jihar ta Borno, ya kuma yi kira akan ‘yan Najeriya da su zauna da juna lafiya ba tare da yin la’akari da bambance-bambancen addini, ƙabilanci da al’ada a tsakani ba.

Dan sanda ya harbe yaro har lahira akan ya daukar masa ‘Pure Water’ guda 1

Wani fusataccen dan sanda ya harbe wani yaro har lahira, sakamakon jayayya da suka yi akan ruwan leda, a garin Kabba tsohuwa, dake karamar hukumar kabba/Banu cikin jihar Kogi, a safiyar ranar Asabar.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta hada, lamarin ya janyo gagarumin ganganko daga mutanen da suka fusata, abin da ya sa duk alamuran kasuwanci suka tsaya cak a garin da lamarin ya faru.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe