24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

TikTok ya zama bala’i: Bayan rikicin su Suddenly, su Zuhura da Maryam sun kwashi dambe har da cizo

LabaraiTikTok ya zama bala’i: Bayan rikicin su Suddenly, su Zuhura da Maryam sun kwashi dambe har da cizo

Bayan rikicin su Suddenly da Aisha Zaki wanda ya janyo yaran Aisha Zaki suka je har gida suka lakada wa Suddenly dukan tsiya, har ‘yan sanda suka shiga, wani fadan ya kara rikicewa.

A wani bidiyo wanda wata Aisha Bashir ta wallafa a shafinta na Facebook an ga yadda wasu ‘yan mata suke ba hammata iska.

A cikin bidiyon an ji wata tana cewa “abin har da cizo?” yayin da suaran mutane suke kokarin raba fadan ana kiran sunan wata Maryan da Zuhura wadanda fadan ya kacame tsakanin su.

rikicin tiktok2
Bayan rikicin su Suddenly, su Zuhura da Maryam sun kwashi dambe har da cizo

An ji wani a cikin bidiyon yana cewa “Zuhura ku daina ba mutuncin ku bane”.

“Har ila yau, Zuhura wacce ke sanye da wata roga mai ruwan hoda tana ihu tana cewa:

“Manaja! Zo ka fitar min da wannan da ta shiga inda nake.”

Mutane da dama sun zargi cewa a Otal fadan ya auku wanda rikicin TikTok ya fada hada Zuhura da Maryam din kuma alamu suna nuna cewa kowa ya san kowa a cikin su.

Bidiyon ya dauki hankalin mutane wadanda suka din cece-kuce suna alawadai da irin wannan masifar da TikTok ta zama a arewa tunda daga su Suddenly har wadannan Hausawa ne.

Labarun Hausa ta tattaro wasu daga cikin tsokacin da jama’a su ka yi karkashin bidiyon wanda fiye da mutane 200 suka dinga maganganu akai:

Wani Abubakar Adamu yace:

“Yaran hausawa sun matukar lalacewa yanzu.. Ya Allah Ka shirya mana zuri’a. Amin. Sun hada kansu da ‘yan daudu da kawalai sun maida kansu ‘yan kasuwa.”

Zara Mimi Ahmed tace:

“Ya salam. Wai don Allah wannan ba abun kunya bane. Nikam basu da iyaye ne da zasu masu fada irin wannan abun da suke yi. Sam ko kunya ma basu ji wallahi.”

Musa L Maje yace:

“Wannan wacce irin rayuwa ce? Dana sanin yana gaba.”

Sani Umar yace:

“Wanda ya dauki hoton shi ne tsinanne dama can basu san darajar junansu ba.”

zTirkashi: ‘Yan matan TikTok sun yi bidiyo su na lakada wa abokiyar harkallarsu bakin duka

Tirkashi: ‘Yan matan TikTok sun yi bidiyo su na lakada wa abokiyar harkallarsu bakin duka

An samu bayanai akan budurwar wacce aka je har gida aka lakada mata duka, Mai suna Suddenly, cewa wani rikici ne ya hada su da ita, hakan yasa su ka yanke shawarar binta har gida su yi mata dukan tsiya.

Tuni bidiyon ya karade shafukan sada zumuntar zamani inda kowa ya ke ta tofa albarkacin bakinsa.

Kamar yadda kowa ya sani, Kafar TikTok ya tashi daga wurin sada zumunta, inda ya koma wurin barar da mutunci.
Zaka ga babbar mace babu hijabi a jikinta tana kwasar rawa na rashin daraja. ‘Yan daudu ma ba a barsu a baya ba, zaka ga su na musayar bidiyo na zage-zagen juna tsakaninsu.

Tuni dama mutane su ka fara bukatar a rufe kafar TikTok saboda tabarar da ake gwabzawa kuma yana lalata tarbiyyar yaran jama’a.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe