34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Budurwa ‘yar Najeriya ta ɗau hankulan mutane bayan ta zagaye jihohi 22 akan babur cikin kwana 7 kacal

LabaraiBudurwa 'yar Najeriya ta ɗau hankulan mutane bayan ta zagaye jihohi 22 akan babur cikin kwana 7 kacal
  • Wata budurwa ‘yar Najeriya, Fehintoluwa Okegbenle, ta karade jihohi 22 bisa babur a yawon buɗe ido.
  • Budurwar ta bayyana cewa ba ta fuskanci matsalar tsaro ba yayin da take tafiya a yankunan Arewacin ƙasar nan
  • ‘Yan Najeriya da dama sun bayyana ra’ayin su inda su ka yaba mata bisa wannan namijin ƙoƙarin da tayi

Wata budurwa ‘yar Najeriya, Fehintoluwa Okegbenle, ta yi tafiyar yawon buɗe ido a Najeriya, inda ta zagaye har zuwa jihohi 22 a bisa babur.

Budurwa
Fehintoluwan a yayin tafiyar ta ta. Hoto daga @FehinLean

Da ta ke bayar da labarin ta a Twitter, budurwar ta bayyana cewa ta kammala tafiyar cikin sati ɗaya. A cikin kwanaki bakwai, ta zaga jihohi irin su Ogun, Edo, Enugu, Kaduna, Kano, Bauchi, da sauran su.

Budurwar ta bayyana ba ta fuskanci ƙalubalen tsaro ba yayin tafiyar ta

Fehintoluwa ta wallafa wasu hotuna a shafin sada zumuntar inda ta bayyana cewa taji daɗin tafiyar sosai.

Da take amsa tambayoyi kan yadda ta samu ta tsallake jihohin arewacin ƙasar nan da ake fama da rashin tsaro, ta bayyana cewa tayi saa bata fuskanci matsala ko ɗaya ba.

Ta ƙara da cewa tana la’akari sosai da dukkanin abinda ba ta gamsu dashi ba akan hanya. Kafin ta bi hanya, tana haɗa bayanai akan hanyar kwana guda kafin ta bi hanyar.

Nayi mamakin yadda na zagaye Najeriya akan babur dina, jihohi 22 a cikin kwana bakwai.

Lagos, Ogun, Oyo, Osun, Ekiti, Kogi, Abuja, Kaduna, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Benue, Cross River, Ebonyi, Enugu, Anambra, Delta, Edo, Ondo, Ogun, Lagos.

Naji dadi sosai, wannan yawon bude ido ne mai cike da abubuwan al’ajabi.

Mutane sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan lamari

Wallafar da tayi, ta janyo mutane da dama sun bayyana ra’ayoyin su. Ga ƙadan daga ciki:

@stgorzhye ya rubuta cewa

Ya ki kayi wajen wuce yankunan arewacin Najeriya masu fama da masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga

@imitoriyin ya rubuta

Mace ce ke. Kina nufin ‘yan bindiga ba su kai miki hari akan hanya ba?

@lord_barns ya rubuta

Jihohi 22 cikin kwanaki bakwai? Duk girman arewa kin zagaye ta tare da wasu jihohin? Da ace babur ɗin ki na magana, da ya faɗi baƙar wahalar da yasha

@blessmich85 ya rubuta

Gaskiya ke ta daban ce. Na yaba wa jarumtar ki.

Matashi da ya samu A takwas a WAEC, ya kammala digiri da sakamako mai daraja ta ɗaya a jami’a

Wani matashi ya nuna sakamakon jarabawar WAEC da jami’a bayan ya kammala karatun digiri ɗinsa na farko a fannin injiniyanci

‘Yan Najeriya da dama da suka shiga shafinsa na Twitter sun yaba da kokarinsa yayin da wasu ke ba shi shawarar da ya yi aiki don samun kwarewa ta fannin kasuwanci ganin cewa ya kammala karatunsa da 4.86 CGPA, wata kungiya mai zaman kanta a Amurka ta yi masa magana idan ya na son tallafin karatu.

Wani matashi dan Najeriya, Olowookere Victor Oluwaferanmi, ya shiga kafafen sada zumuntar zamani don baje kolin manyan nasarorin da ya samu a fannin ilimi a tsawon shekaru.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe