24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Obasanjo Ya fito yayi magana kan kone gonarsa da ake zargin ‘yan bindiga sunyi a jihar Benue

LabaraiObasanjo Ya fito yayi magana kan kone gonarsa da ake zargin 'yan bindiga sunyi a jihar Benue
  • Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasnajo, ya bayyana cewa barnata gonakinsa tare da konasu ba karamar asara ba ne ga cigaban kasa
  • Obasanjo ya ce ya yaba da kokarin da gwamnatin jiha da kananan hukumomi su ke yi wajen daukan matakin zakulo wanda ake zargi da aikata wannan aika-aika
  • Tsohon shugaban kasar ya ce ya yi matukar farin ciki da cewa ba a rasa rai ba yayin da aka kai harin a gonar mangoron na sa mai girman hekta 2,420

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya mayar da martani kan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa gonarsa da ke Hawe a yankin Aliade a karamar hukumar Gwer ta Gabas ta jihar Benue.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasar ya ce barnata tare da kona masa gonakin sa mai fadin hekta 2,420, mummunar koma baya ne.

A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi, ya fitar a Abeokuta, jihar Ogun, Obasanjo ya ce gwamnati tun daga kan matakin jiha zuwa kananan hukumomi sun yi ruwa da tsaki game da faruwar lamarin.

Obasanjo yayi magana kan kone gonarsa da aka yi
Obasanjo yayi magana kan kone gonarsa da aka yi

Babu wani tashin hankali saboda yana da yakinin cewa gwamnati zata zakulo wadanda suka aikata laifin.

Babu rai daya salwanta

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, duk da asarar da harin ya janyo, abin farin cikin shine babu rai ko daya da ya salwanta.

Gidan Talabijin na Channels sun ruwaito cewa shugaban karamar hukumar da lamarin ya akfu ya shaidawa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom cewa gonar mangwaro mai fadin hekta 2,420 ta Obasanjo ta kone tas.

Kusan rabin gonar ya kone

Emmanuel Otserga ya ce sama da rabin gonar mangwaro da ke da fadin hekta 139 aka kona, wasu da ake zargin barayi ne suka aikata wanan aika aika.

Ya kara da cewa, bayan faruwar lamarin, an kama wasu mutum hudu da ake zargi, sannan kuma ana ci gaba da zakulo sauran wadan da suka aikata laifn don ganin an gurfanar da su gaban kuliya.

Otserga ya ce:

Daga ganin yanda gobarar ta tashi an cinna wutar ne da gangan. Saboda Gidan gona yana da tsaro sosai, babu yadda za a yi wuta ta tsallako daga wani wuri ta zo ta cimma cikin gonar”.

Gwanatin jihar Binuwai ta umurci a tsaurara bincike

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya yi matukar nuna alhini ga me da gobarar da ta tashi a gonar tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Gwamnan ya bayyana bakin cikinsa kan lamarin, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 1 ga watan Fabrairu a garin Markurdi, babban birnin jihar. A cewarsa, sun umarci jami’an tsaro da su bi diddigin wadanda suka aikata wannan aika-aika domin gurfanar da su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe