34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ana yiwa ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya barazanar kisa saboda sun sha kasa a wasan AFCON

LabaraiAna yiwa 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya barazanar kisa saboda sun sha kasa a wasan AFCON

Korar Najeriya da ƙasar Tunusia tayi a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON), a zagaye na 16, babban abin takaici ne a wajen magoya bayan ƙungiyar.

Ba kawai ana fatan kungiyar Super Eagles tayi nasara kawai a wasan bane, amma ana yiwa ƙungiyar kallon wacce zata iya kaiwa har zuwa wasan ƙarshe a gasar inda ake sa ran zata goge raini da ƙasar Kamaru mai masaukin baki.

Dalilin samun wannan ƙwarin guiwar ya samo asali ne yadda tawagar tayi abun kirki a wasannin ta na ukun farko inda ta samu maki tara, sannan ta zura aƙalla kwallo biyu a kowane wasa.

Sai dai ci ɗaya mai ban haushin da Najeriya ta sha, ya zama lokaci na farko da ƙasar ta kasa zuwa zagaye na gaba da zagayen 16 na gasar ta AFCON tun shekarar 1984

Wasu daga cikin ‘yan wasan sun sha suka sosai

Mutane da dama sun ɗauki abin da zafi sosai. Mutum biyu daga cikin ‘yan wasan sun sha suka sosai inda akai musu zagin cin mutunci.

'Yan Najeriya a wajen wasan AFCON
‘Yan Najeriya a wajen wasan AFCON

Bayan ya kasa tare kwallon da aka zura a ragar sa, mai tsaron gida Maduka Okoye yasha zagi a kafafen sada zumunta inda wasu su ka dinga aibata kamannin sa, sannan kuma da fatan mutuwa kan sa da kuma masoyan sa.

Wani ya bayyana ra’ayin sa ta hanyar yiwa mai tsaron ragar fatar samun haɗarin jirgin sama, yayin da wani kuma yasha mummunan alwashi a kansa idan ya sake ya dawo Najeriya.

Wani daga cikin su yayi fatan ubangiji ya azabtar da iyalan mai tsaron gidan inda ya zarge shi da yin sakaci da gangan.

Hakan ya sanya dole Okoye ya kulle wajen bayyana ra’ayi kan wallafar sa a kafar sadarwa ta Instagram.

Alex Iwobi, wanda aka sanyo bayan hutun rabin lokaci, an bashi jan kati cikin mintuna biyar da sa shi a wasan bayan ya taka kafar wani ɗan wasa. Shima yasha suka sosai a kafar ta yanar gizo wanda hakan ya sanya shi dole rufe duk wata wallafa da yayi a Instagram.

Mai horar da ƙungiyar, Eguavoen, ya shaida wa jaridar Aljazeera cewa:

Yakamata mutane su yi aiki da hankali kada su sauya ɓacin ran su zuwa kalaman tsana da kuma barazana akan wasu ‘yan wasa ba

Waɗannan ‘yan wasan sun yi iyakar ƙoƙarin su ba dalilin dora laifi akan wasu. Akwai matsin lamba wurin bugawa Najeriya wasa, bai yiwuwa ka koma zagi da yin barazana kan wanda yaje kare martabar Najeriya kawai domin kana da ikon hawa yanar gizo. Wannan ba daidai bane ko ƙadan.

Ana zargin ‘yan wasan da nuna rashin kwazo sosai

Wasu suna ganin cewa ‘yan wasan ba su damu da nasarar ƙungiyar ba shiyasa su ke nuna halin ko in kula.

Irin wannan mahangar ne akai ta suka da zagin Okoye wanda aka haifa a birnin Dusseldorf na ƙasar Jamus, sannan kuma ya fara bugawa Najeriya wasa a shekarar 2019.

Hanyoyin da ake bi wajen nuna ɓacin rai ya nuna yadda halayyar magoya baya ta ke a Najeriya gabaɗaya.

Babu wasu tsauraran dokoki da su ke kare mutane daga hantara a kafafen sada zumunta a Najeriya.

Gwamnatin ƙasar dai ta haramta cin zarafi ta kowace irin fuska a yanar gizo a ƙasar.

Bayan shan kashin da ƙasar tasha a hannun Tunisiya, mai horar da ƙungiyar yayi ƙoƙarin sanya wa wutar da ruru ruwan sanyi inda ya ɗora alhakin hakan akan zaɓar ‘yan wasan da yayi da kuma kuskuren alaƙalin wasa.

Sai dai ya san cewa hakan ba zai kore laifin da ake gani ba na ƙungiyar a wajen magoya bayan ta.

A karon farko Ahmed Musa yayi magana bayan an kori Super Eagles daga AFCON

Kyaftin ɗin Super Eagles Ahmed Musa, ya gode wa ‘yan Najeriya bisa ƙaunar da suka nuna wa kungiyar su duk da sun gaza wucewa zagaye na gaba a gasar cin kofin Nahiyar Afrika da ta gudana a ƙasar Kamaru.

Ahmed Musa ya bayyana cewa ‘yan wasan sun yi iyakar ƙoƙarin su, sai dai daga ƙarshe basu samu nasara ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@jamilusman

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe