29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban karamar hukuma tare da wasu mutum 5

Labarai'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban karamar hukuma tare da wasu mutum 5

Wasu ‘yan bindiga sun sace mutane biyar a wurare daban-daban a jihar Ekiti a ranar Litinin 31 ga watan Janairun shekarar 2022.

Wata majiya ta bayyana cewa a harin da ‘yan bindigar suka kai na farko, sunyi awon gaba da tsohon shugaban karamar hukumar Ilejemeje dake jihar Ekiti, Bamgboye Adegoroye, da kuma wani da suke tare dashi a cikin motar shi, inda a hari na biyu kuma sun sace mutane uku da suke aiki a wata masana’antar sarrafa gawayi.

An sace tsohon shugaban karamar hukumar a motarshi tare da abokin shi

A rahoton da jaridar Punch ta ruwaito, shugaban karamar hukumar Ifesowapo, Mr Kayode Akerele, shine ya fara magana akan faruwar lamarin, inda ya ce Adegoroye da wani mutum anyi garkuwa da su a lokacin da suke cikin mota akan hanyar Isan-Iludun ranar Litinin.

An sace shugaban karamar hukuma
An sace shugaban karamar hukuma

Ya ce:

“Mun gano cewa tsohon shugaban karamar hukumar da wani mutum da suke tafiya tare a mota sun shiga hannun ‘yan bindiga a lokacin da suka harbi motar shi. Sun tsaya sakamakon motar su da ta lalace saboda harbin da ‘yan bindigar suka yi musu, inda a wajen suka sace su. Har yanzu bamu da labari idan ‘yan bindigar sun tuntubi iyalan su.

An sace masu aikin sarrafa gawayi a hari na biyu

A hari na biyun shugaban karamar hukumar Ero LCDA, Mr Akin Alebiosu, ya ce an sace mutane uku da suke aikin sarrafa gawayi a Ikun-Ekiti da misalin karfe 6:30 na yamma, duka a rana daya.

Alebiosu ya ce shugaban ma’aikatan da aka bayyana sunan shi da Olu, wanda yake dan asalin garin Ikun-Ekiti, da kuma wasu da lamarin ya shafa suna tsaka da aiki a kusa da kogin Ero a lokacin da lamarin ya afku.

An bukaci jami’an tsaro su dauki mataki a yankunan da lamarin yake faruwa

Shugabannin kananan hukumomin guda biyu sun roki hukumomin tsaro da su dauki mataki akan yankin Ayede-Isan-Iludun-Ikun, saboda yankunan sun fara zama maboyar ‘yan ta’ada.

Haka kuma, kwamandan rundunar Amotekun, Brig Gen. Joe Komolafe (rtd), ya ce rundunar su tana aiki da sauran jami’an tsaro don ceto rayukan mutanen da aka sace.

Komolafe, ya koka kan cewa mutane ne suke bawa ‘yan bindiga labari akan kokarin da jami’an tsaro suke yi, ya ce amma hakan ba zai hana su canja salo ba wajen daukar mataki akan ‘yan ta’addar ba.

‘Yan sanda sun cafke wasu matasan da suka kashe budurwar domin yin tsafin kudi da ita

Jami’an ‘yan sanda sun kama wasu matasa uku da laifin kashe wata budurwa domin yin tsafin kudi da ita a jihar Ogun

An kama su ne bayan wani jami’in tsaro ya gansu suna kona wani abu da ake tuhuma wanda ya zama kan mutum a cikin wata tukunya

A halin yanzu, jami’an ‘yan sanda na ci gaba da neman mutum na hudu wanda ake zargi da zama saurayin wacce aka kashe.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama wasu matasa hudu da laifin kashe budurwar daya daga cikin matasan saboda su yi tsafin kudi da ita.

A cewar sanarwar da Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ‘yan sandan suka samu a ranar Asabar din da ta gabata a hedikwatar yankin Adatan daga hannun shugaban jami’an tsaro na al’umma, cewa an ga wadanda ake zargin suna kona kan mutum a cikin tukunya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe