24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin tono gawar wani Almajiri da ya mutu saboda tsananin azabar da yake sha a wajen Malamin shi

LabaraiGwamnatin jihar Kano ta bada umarnin tono gawar wani Almajiri da ya mutu saboda tsananin azabar da yake sha a wajen Malamin shi

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci a tono gawar wani Almajiri, wanda ake zargin Malamin shi ya kashe shi saboda tsabar azabtarwa.

Dr Muhammad Tahar Adamu, kwamishinan harkokin addini na jihar, shine ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara makarantar dake unguwar Wailari cikin jihar ta Kano, a jiya Talata 1 ga watan Fabrairu.

An kama wasu da ake zargin su da hannu a kisan almajirin

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce tuni sun kama wasu da ake zargin da hannu a lamarin, rahoton Daily Trust

Ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan sun kuma kai wani sumame gidan gyaran hali na bogi da aka bude a unguwar Naibawa ‘Yan Lemo, cikin karamar hukumar Kumbotso.

An gano gidan gyaran hali na bogi

Da misalin karfe 11 na rana, mun samu rahoto daga gurin wasu mutane 10 da suka samu suka kubuta daga gidan gyaran halin, cewar wani mai suna Musa Safiyanu, mai shekaru 55, dake unguwar Naibawa ‘Yan Lemo, karamar hukumar Kumbotso, cikin jihar Kano, shine ya mallaki wannan wajen gyaran hali na bogi, inda yake daure mutane da sarka yana azabtar da su.

Haka kuma sun bayyana cewa wani mai suna Aminu Ado, mai shekaru 22, mazaunin Naibawa Quarters, ya rasa ransa a ranar 29 ga watan Janairun shekarar 2022, sakamakon azabar da ya sha a hannun Abdulladif Musa mai shekaru 18, mazaunin Naibawa Wailari Quarters.

Bayan mun karbi wannan rahoto, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya tada rundunar ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Abdulkarim Abdullahi, domin suje suyi bincike akan lamarin su tabbatar da idan gaskiya ne, sannan kuma su kama wadanda ake zargin.

Cikin kankanin lokaci rundunar ta bazama, kuma suka gano cewa wannan magana gaskiya ce.

Almajiri
Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin tono gawar wani Almajiri da ya mutu saboda tsananin azabar da yake sha a wajen Malamin shi

An samu nasarar ceto mutum 113 daga gidan

Ya kara da cewa, a ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2022, an samu nasarar ceto mutum 113 daga wannan waje, wadanda aka kulle a cikin daki.

Wasu da aka samu da raunika a jikinsu sakamakon azabar da suka sha, an garzaya da su zuwa Asibitin Murtala domin duba lafiyar su, haka kuma an mika su zuwa ga gwamnatin jihar Kano, inda kuma aka kama mutum 6 wadanda ake zargi da wannan aika-aika, ga sunayen su kamar haka; (i) Musa Safiyanu, Na’ibawa Yan Lemo Quarters, Kano, (ii) Abdullatif Musa, mai shekaru 18, Na’ibawa Wailari Quarters, Kano, (iii) Usman Abdulrauf Imam, mai shekaru 19, wanda ya fito daga unguwar Yanya dake babban birnin tarayya Abuja, (iv) Mustapha Bala, ‘mai shekaru 20, wanda ya fito daga garin Azare, jihar Bauchi, (v) Sadiq Ismail, ‘mai shekaru 19, Unguwa Uku Quarters, Kano, (6) Umar Bako Abdulwahab, mai shekaru 38, Kureken Sani Quarters, Kumbotso LGA Kano.

Bayan gabatar da bincike, wadanda ake zargin sun bayyana cewa, sun shafe sama da shekaru 10 suna wannan abu, duk da haramta hakan da gwamnatin jihar Kano ta yi,” a cewar shi.

Sun shafe sama da shekara 10 suna azabtar da al’umma

Wannan dai na zuwa ne bayan kisan Hanifa Abubakar, yarinyar ‘yar shekara biyar, da malamin ta Abdulmalik Tanko, ya yi.

Abdulmalik Tanko dai ya sace Hanifa ne daga gidansu kafin daga baya ya kashe ta.

Ba zan bata lokaci ba wajen sanya hannu akan hukuncin kisan da za a yankewa wanda ya kashe Hanifa – Ganduje

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ba zai bata lokaci ba wajen sanya hannu akan hukuncin kisan da za a yankewa Abdulmalik Tanko, idan har kotu ta gama bincike ta kuma bada dama.

Tanko, wanda yake Malamin Makarantar Noble Kids Academy a cikin karamar hukumar Nasarawa cikin Kano, ya bayyana cewa shi ya kashe Hanifa Abubakar, wacce ya sace ta daga gidansu a cikin watan Disambar shekarar 2021.

A ranar Litinin 24 ga watan Janairu, gwamnan yayi alkawarin bin duk wata doka da ta bashi damar sanya hannu don yankewa Tanko hukuncin kisa, matukar kotu ta amince da hakan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe