27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Daga karshe, Sadiya Haruna ta hakura da zaman Kano bayan an kusa watsa mata ‘Acid’

LabaraiKannywoodDaga karshe, Sadiya Haruna ta hakura da zaman Kano bayan an kusa watsa mata ‘Acid’

Fitacciyar mai sayar da maganin mata a garin Kano, ‘yar asalin Maiduguri, Sadiya Haruna ta bayyana shirin ta na komawa Jihar Borno, tushen ta.

Tun ranar Juma’ar da ta gabata ake ta tirka-tirka har kafafen sada zumuntar zamani suka dauki zafi bayan Sadiya Haruna ta wallafa bidiyon ta tana ihu tare da kuka yayin da take bayani.

A cikin bidiyon ta bayyana sanye da wani hijabi wanda ta yi cikin mota tana neman taimako inda tace bata san inda dan’uwanta yake ba.

Sadiya Haruna ta shaida yadda wasu maza suka bi ta zasu watsa mata ‘acid’ bayan ta tashi daga shagonta ta zarce siyayya.

sadiyya haruna
Sadiya Haruna zata koma Maiduguri.

Sai dai ta tsallake rijiya da baya bayan ta ji lokacin da daya yake cewa “mu watsa mata mu gudu”, wanda hakan yasa ta yi sauri ta shiga motarta ta rufe.

Sadiya Haruna ta shaida yadda suka ci gaba da binta wanda tace tana tsoron sun ga wucewar dan’uwanta daga bisani suka koma bin shi. Can kuma tace sun kai dan’uwan nata ofishin ‘yan sanda kamar yadda ‘Besty’ dinta ya tabbatar mata.

Daga bisani dan’uwanta da abokin wanda take kira da ‘Besty’ suka bayyana suna neman ta hankali a tashe, sai can ta fito tace ta boye ne don gudun su Teema Makamashi da sauran abokan rikicin ta su kai mata farmaki.

Ta ce su take kyautata zaton suna farautar ran ta.

Sai dai daga bisani, Chizo Germany, wanda kowa ya san abokinta ne ya wallafa wata murya a shafinsa na Facebook inda yace Sadiya Haruna zata hakura da zaman Kano.

Kamar yadda idan mutum ya saurari muryarta zai ji tana bayyana yadda ta tattauna da iyayenta ‘yan Maiduguri, inda ta ce sun ce ta koma can.

Ta bayyana yadda zaman ta a Kano yake taimaka wa sana’arta amma a cewarta mahaifiyarta ta ce ta hakura Ubangiji zai rufa asiri.

Sadiya Haruna ta ce zata wuce garin su kuma akwai yuwuwar a daina jin duriyarta a kafafen sada zumunta saboda farautar ran ta da wasu suke yi.

Sabuwar rigima kan bidiyon tsiraici, Sadiya Haruna na barazanar tona Asiri, Tema Makamashi tayi harbin iska

Wata sabuwar rigima ta kacame tsakanin sayyada Sadiya Haruna da kuma jarumar Kannywood, Teema Makamashi kan bidiyon tsiraici, duk da dai su biyun ba su ambaci sunan juna ba.

Su biyun sun bayyana a shafukansu na kafafen sada zumunta su na sakin bidiyoyi tare da habaice-habaice, ganin yadda kalaman nasu su ke zama martani ga juna yasa mutane su ka fahimci cewa fadan tsakaninsu ne, kuma dama su na da wata jikakkiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe