35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Matan Najeriya sun kafa tarihi, sun fi ko wanne mata a nahiyar Afirki yin bilicin, Bincike

LabaraiMatan Najeriya sun kafa tarihi, sun fi ko wanne mata a nahiyar Afirki yin bilicin, Bincike

Binciken da CNN ta gudanar ta janyo cece-kuce iri-iri a kafafen sada zumuntar zamani dangane da bilicin.

Binciken na CNN kamar yadda Gossip.com ta ruwaito ya nuna cewa matan Najeriya sun fi ko wanne mata a nahiyar Afirka siyan man sauya launin fata.

Mayukan bilicin sun fi kasuwa da kaso 75% saboda yadda matan Najeriya suke tururuwar zuwa siyan su.

Daga Najeriya sai matan Senegal ne suka fi ko wanne mata siyan mayukan da kaso 60% duk don komawa fararen fata.

An bayyana yadda binciken na CNN ya gudana kamar haka:

Matan Najeriya sun kafa tarihi, sun fi ko wanne mata a nahiyar Afirki yin bilicin, Bincike
Matan Najeriya sun kafa tarihi, sun fi ko wanne mata a nahiyar Afirki yin bilicin, Bincike

Abubuwan da mata suke amfani da su wurin sauya launin fatar nasu sun hada da mayuka, sabulai, allurai da sauran su.

Bilicin yana janyo matsaloli da dama a jikin dan Adam wanda ciki akwai cutar daji (Cancer) wacce take lalata fatar jikin mutum.

Akwai alamomi da dama da ake gane mutum idan ya kasance mai bilicin, akwai bayyanar tabbai a gabobi kamar na hannu, guiwa da sauran su.

Manyan dalilan da su ke jefa mutane harkar Bilicin

Masana sun dade su na nuna illolin da ke tafe da sauya launin fatar dan Adam wanda ake kira da harkar bilicin.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, akwai dalilan da su ke sa mutane su na shiga harkar mai hadarin gaske.

Suka ko kuma kushe ga halitta musamman ga mutane masu duhun fata ya kan tunzura su harkar bisa ruwayar Daily Trust.

Shin ka taba ko kin taba kallo wani ki ka kira shi da baki fentin Allah? Bulaki? Da sauran miyagun sunaye da ake alakantawa ga bakake?

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe