27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Abinda yasa na rabu da Atiku Abubakar – Tsohuwar matar Atiku Jennifer ta bayyana dalilin rabuwar su

LabaraiAbinda yasa na rabu da Atiku Abubakar - Tsohuwar matar Atiku Jennifer ta bayyana dalilin rabuwar su

Ɗaya daga cikin matan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, Jennifer (Jamila) Douglas, ta tabbatar da mutuwar auren su ita da Atiku Abubakar inda ta bayyana dalilin aukuwar hakan.


Atiku shine ɗan takarar shugabancin ƙasa a zaben 2019 ƙarƙashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A wata takarda da jaridar Leardership ta samu ranar Talata, Jennifer ta bayyana cewa ba ta nemi Atiku ya sawwake mata ba saboda ya ƙara auro wata matar.

Ta kuma ƙara fashin baƙi akan wasu lamura da su ka wakana a tsakanin ta da tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

Saboda ya ƙaro sabon aure ba shine abinda ya kawo saɓani ba a tsakanin mu kamar yadda wasu ke yayatawa. Musulmi ne kuma ban taɓa adawa da matan sa ba ko niyyar sa ta ƙara aure. a cewar ta

Ta bayyana babban dalilin rabuwar su da Atiku Abubakar

A cewar ta, wasu daga cikin abokan Atiku sun yi ƙoƙarin sulhunta su amma hakan bai yiwu ba.

Ta bayyana cewa:

Babban dalilin rabuwar auren mu shine cigaba da zama da na keyi a ƙasar Ingila da kuma wasu saɓani da su ka daɗe a tsakanin mu.”

Atiku Abubakar yayi ƙoƙarin kwace wata kadara a hannun ta

Haka kuma Jennifer ta yi iƙirarin cewa Atiku yayi yunƙurin kwace wata kaddara da ya mallaka mata a baya. Inda ta ƙara da cewa yanzu haka ana sharia akan kadarar a Dubai.

A lokacin da ake yunƙurin sasanta mu, ya ƙaryata cewa ya bani kyautar gidan (gidan auren mu na Asokoro) duk da na nuna masa takardu waɗanda su ke ɗauke da sa hannun mai taimaka masa. Ya buƙaci da na mayar masa da kyautar sa.

Da na tambaye shi ko a ina ni da yaran zamu zauna idan mu ka dawo Najeriya? sai ya faɗa min cewa tunda ni na nemi da ya sake ni, sai naje ne nemi wurin da zan zauna, sannan daga baya na fice na bashi wuri .”

Har ya zuwa yanzu da ake haɗa wannan rahoton, Atiku bai ce komai ba dangane da wannan lamarin.

Babban yaron Atiku Abubakar ya ajiye tafiyar Atiku ya koma jam’iyyar APC tare da dumbin magoya bayansa

Mataimakin shugaban hadinkan matasan jamiyyar PDP ta Arewa maso gabas, Muhammad Abdul Babangida, ya bar jamiyyar PDP shi da magoya bayansa, inda ya koma APC jamiyya mai ci, a jihar Yobe.

Jim kadan bayan ya fita, Babangida ya shaidawa jaridar Leadership cewa, jamiyyar PDP bata yi da shi da magoya bayansa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@jamilusman

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe