24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Dillalin gidaje ya sheƙa barzahu a ɗakin otal bayan yayi lalata da matar aure

LabaraiDillalin gidaje ya sheƙa barzahu a ɗakin otal bayan yayi lalata da matar aure

Wani dillalin gidaje Diran Elijah mai shekaru 50 a duniya ya rasa ransa bayan yayin lalata da tsohuwar matar sa mai suna Idowu a wani ɗakin Otal a unguwar Agbbado a jihar Ogun.

Idowu, wacce ta sake sabon aure har ta haifi yara biyu dai ta rabu da Elijah shekaru huɗu da su ka gabata.

Ogun State mappp
Dillalin gidaje ya sheƙa barzahu a ɗakin otal bayan yayi lalata da matar aure

City Round ta samu cewa su biyun sun yarda za su haɗu ne a Otal ɗin da misalin ƙarfe 10 na dare ranar Lahadin da ta wuce bayan Elijah ya kira ta a waya.

Elijah yana cikin hutawa bayan kammala lalatar kawai sai ya yanke jiki ya faɗi.

Kafin matar ta yi yunƙurin sanar da ma su otal har Elijah ya garzaya barzahu.

Wani mazaunin unguwar mai suna Afolabi ya ifaɗawa PUNCH cewa lamarin ya tada hankalin jama’ar unguwar yayin da ‘yan sanda su ka dira domin gudanar da bincike.

“Mai otal ɗin yayi niyyar yin ƙarya cewa mutumin a waje ya faɗi ya mutu. Amma matar (Idowu) ta ce ƙarya ne, sun yi jima’i ne sai yayi korafin ya gaji yana son hutawa. Bayan wani ɗan lokaci sai ya daina numfashi.

Ta kira ma’aikatan otal ɗin amma tuni har rai yayi halin sa. Daga baya na samu cewa sun taɓa yin aure a baya amma sun rabu.” a cewar sa

Wata majiya ta kusa da matar ta shaida wa City Round cewa matar ta ƙarbi bashin banki ne wanda ta kasa biya. Majiyar ta cigaba da cewa Elijah ya gayyace ta otal ɗin sannan yayi mata alƙawarin biyan wani kaso na bashin.

“Sun taɓa yin soyayya a baya. Suna da yara biyu a baya amma sun rasu. Daga baya sun rabu inda kowanne ya sake sabon aure. Ta karɓi bashin banki ne wanda ta kasa biya. Bankin ya ƙwace gidan da take ciki yanzu ita da mijinta a Ifo inda ta koma kwana a cikin coci.

“Elijah ya tuntuɓe ta inda yayi mata alƙawarin zai bata kuɗi ta biya wani kaso na bashin. Ya rasu bayan sun yi jima’i. ‘Yan sanda sun ɗamke ta amma’yan’uwan mutumin sun ce ba su buƙatar yin shari’a da ita.”

Haka kuma wata majiya ta sanar da cewa mamacin da Idowu sun taɓa aure a baya, inda yayi nuni da cewa ‘yan sanda sun kasa gano ko akwai hannun matar a mutuwar sa.

“Idowu matar sa ce da su ka haifi yara biyu a tare. Sun rabu shekaru huɗu da su ka wuce. Matar ta sake aure inda ta haifi yara biyu. Mutumin shima ya sake aure inda ya haifi yaro ɗaya. Baa daɗe ba ya kai matar sa garin su Ilesa a jihar Osun.

“Ya samu lambar wayar tsohuwar matar ta sa inda ya nemi da ta kawo masa ziyara. Sun je otal, bayan sun yi jima’i sai ya daina motsi. Ya mutu kafin a fitar da shi daga otal ɗin. An kai gawar sa garin su (Ilesa). ‘Yan’uwan sa sun ce ba su buƙatar kai maganar gaban kotu. An bada belin matar.” a cewar majiyar

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yayi nuni da cewa tuni iyalan biyu su ka sasanta lamarin a tsakanin su.

An kama wani katon gardi da yayi shigar mata yaje ya kashe dan gidan matar shi da wuka

‘Yan sanda sun kama wani mutumi dan shekara 30, mai suna Shawn Bobb, wanda aka kama shi da hannu a kisan dan gidan matarshi a Guyana.

Helkwatar ‘yan sanda ta Guyana ta bayyana sun kama Bobb a gidan dake Helena dake lamba 1 a Mahaica, da misalin karfe 7 da minti 20, ranar Asabar 29 ga watan Janairu.

Yayi kokarin guduwa sanye da kayan mata

A lokacin da ‘yan sanda suka isa wajen, sun hango Bobb yana kokarin guduwa ta daya daga cikin tagogin gidan, inda yayi shiga irin ta mata, yayi kwalliya ya sanya gashin mata a kan shi.

A yanzu haka dai Bobb na hannun jami’an ‘yan sanda dake Georgetwon, inda suka kai shi asibiti domin duba lafiyar shi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: 

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe