27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Tsananin yunwa ya sanya mutane cin ganyen bishiyoyi domin su rayu a kasar Yemen

LabaraiTsananin yunwa ya sanya mutane cin ganyen bishiyoyi domin su rayu a kasar Yemen

Tsananin yunwar da mutane ke fama da shi a kasar Yemen, ya sanya da dama na cin ganyen bishiya domin su rayu, kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana…

Wani rahoto da fannin kididdigar abinci na majalisar dinkin duniya (WFP) ya fitar a ranar Lahadi, ya nuna cewa akwai mutane da yawa da suke fama da matsananciyar yunwa a kasar Yemen, inda hakan ya sanya dole suke cin ganyen itatuwa domin su rayu sakamakon yakin da suke ta faman yi da kasar Saudiyya wanda ya fara shafar rayukan mutanen da basu ji ba basu gani ba.

WFP ta bayyana cewa matsalar yunwar na cigaba da karuwa a kasar ta Yemen sakamakon rikicin da kasashen na Larabawa ke fama dashi da kuma matsalar tattalin arziki.

WFP sun nuna hoton yadda mutane ke cin ganyen bishiya

Da suke wallafa rubutu mai dauke da hoto a shafinsu na Twitter, WFP sun nuna hoton yadda mutane ke dafa ganyen bishiya wanda suke ci, WFP sun bayyana cewa wuraren da lamarin yafi shafa, irin su Hajjah, dake yankin Arewa maso Yammacin Yemen, suna tafasa ganyen bishiya su ci domin su rayu.

Yemen

Ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta bayyana cewa a farkon watanni shida na shekarar 2018, jihar Hajjah ta samu kimanin mutane 17,000 da suke fama da matsannaciyar yunwa.

Alamun yunwa ya fita karara a jikin al’umma

Matsalar yunwar da ta shafi yankin ta fito karara a jikin al’umma, a cewar wani mazaunin yankin, inda kwayar idon mutane fitowa sosai, fatar jikinsu take tattarewa da dai sauran alamu dake nuni da cewa mutum na fama da yunwa.

A watan da ya gabata, kungiyar jin kai ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa rashin kudi ne ya sanyata ta rage kaiwa kasar ta Yemen tallafin abincin, inda suka fara a watan Janairun da ya gabata.

A rahoton da WFP ta fitar, sama da mutum miliyan 16, wanda yake kimanin rabin al’ummar kasar ta Yemen, suna fama da matsananciyar yunwa, inda kuma yara kimanin miliyan 2.3 suke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.

Tun shekarar 2014 ake fama rikici a Yemen

Kasar ta Yemen dai na fama da matsalar rikici tun a shekarar 2014 zuwa yanzu, a lokacin da kasar Iran ta hada kai da ‘yan kungiyar Houthi suka kwace wani bangare na kasar, ciki kuwa hadda babban birnin kasar Sanaa.

Shigar kasar Saudiyya cikin rikicin domin dawo da zaman lafiya kasar, ya sanya lamarin ya cigaba da ta’azzara, inda hakan ya zama daya daga cikin manyan matsaloli na aikin jin kai da majalisar dinkin duniya ta taba fuskanta, majalisar ta bayyana cewa kimanin kashi 80 cikin dari na kasar suna bukatar tallafi, yayin da mutane miliyan 13 kuma suke fama da matsananciyar yunwa.

An kai wani farmaki a maƙabartar musulmai a kasar Jamus

An kai hari wata maƙabartar musulmai a birnin Iserloun, na ƙasar Jamus, inda aka lalata ƙaburbura da dama.

Yayin harin, wanda ya auku a lokacin bikin sabuwar shekara, wasu mutane biyar da ba a san ko su waye ba, sun farfasa ƙaburburan musulmai inda su ka lahanta maƙabartar da ke birnin Iserloun.

A ranar Asabar ‘yan sanda da masu bincike sun sanar da cewa, kusan ƙaburbura talatin aka rushe sannan aka lalata fulawoyin kwalliyar rukunin musulmai na babbar maƙabartar Iserloun.
Lamarin ya auku ne tsakanin yammacin ranar Juma’a zuwa safiyar ranar sabuwar shekara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe