34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

‘Yan sanda sun cafke wasu matasan da suka kashe budurwar domin yin tsafin kudi da ita

Labarai'Yan sanda sun cafke wasu matasan da suka kashe budurwar domin yin tsafin kudi da ita

Jami’an ‘yan sanda sun kama wasu matasa uku da laifin kashe wata budurwa domin yin tsafin kudi da ita a jihar Ogun

An kama su ne bayan wani jami’in tsaro ya gansu suna kona wani abu da ake tuhuma wanda ya zama kan mutum a cikin wata tukunya

'Yan sanda sun cafke wasu matasan da suka kashe budurwar domin yin tsafin kudi da ita
‘Yan sanda sun cafke wasu matasan da suka kashe budurwar domin yin tsafin kudi da ita

A halin yanzu, jami’an ‘yan sanda na ci gaba da neman mutum na hudu wanda ake zargi da zama saurayin wacce aka kashe
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama wasu matasa hudu da laifin kashe budurwar daya daga cikin matasan saboda su yi tsafin kudi da ita.

A cewar sanarwar da Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ‘yan sandan suka samu a ranar Asabar din da ta gabata a hedikwatar yankin Adatan daga hannun shugaban jami’an tsaro na al’umma, cewa an ga wadanda ake zargin suna kona kan mutum a cikin tukunya.

“Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama wasu matasa hudu da laifin kashe wata budurwa.
Bayan samun labarin, shugaban ‘yan sandan yankin Dapo Adatan, SP Abiodun Salau, ya jagoranci jami’ansa cikin gaggawa zuwa wurin, inda aka kama mutanen uku, yayin da na hudu wanda saurayin yarinyar da aka kashe ya tsere,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.


A yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa cewa abin da suke konawa a cikin tukunyar kan budurwar shugabansu ne wanda ya tsere.

“Sun kara da cewa yarinyar da aka bayyana sunan ta da Rofiat, saurayin ta mai suna Soliu ne ya yaudare ta, inda suka kashe ta da hudu daga cikin su, kuma suka yanke kai suka kwashe gawar a cikin buhu, suka jefar da ita a cikin wani tsohon gini. “

Daga baya sun jagoranci ‘yan sanda zuwa ginin, inda aka tsinto gawar da aka yanka, an ajiye ta a dakin ajiyar gawa na babban asibitin domin a tantance gawarwakin. An kuma gano guntun yankan da wuka da aka yi amfani da shi wajen yanke mamacyar.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Lanre Bankole, wanda ya bayyana matakin da wadanda ake zargin suka dauka a matsayin rashin kunya, ya bayar da umarnin gudanar da gagarumin farautar saurayin budurwar da aka kashe mai suna Soliu.

CP ya kuma bayar da umarnin mika wadanda ake zargin nan take zuwa sashin binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi da nufin gurfanar da su a gaban kotu da wuri.
Rundunar ‘yan sandan ta ce bayan umarnin da kwamishinan ‘yan sandan ya bayar na tabbatar da cafke saurayin marigayiyar mai suna Soliu Majekodumi mai shekaru 18, an kama shi.

‘Yan sanda sun kama wani matashi yana lalata da akuya a jihar Jigawa

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawan Shisu ya sanarwa da manema labarai cewa rundunar su ta samu nasarar cafke wani matashi dan shekara 25 a unguwar Kunnadi dake cikin karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa, yana lalata da akuya.

Jami’an ‘yan sandan sun samu nasarar cafke matashin ne a daidai lokacin da yake aikata masha’a da akuyar.

An ruwaito cewa saurayin ya kama akuyar da karfin tsiya ne ya fara lalata da ita har zuwa lokacin da jami’an tsaron suka iske shi turmi da tabarya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa tuni sun fara gudanar da bincike kan wannan lamari, kuma da zarar sun kammala hada bayanai akan binciken za su tisa keyarsa zuwa gaban kotu don ya girbi abinda ya shuka.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe