27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Labari mai dadi: An rage farashin aure a Dawakin Tofa, jihar Kano

LabaraiAl'adaLabari mai dadi: An rage farashin aure a Dawakin Tofa, jihar Kano

A yayin da samari da dama suke korafi akan yanayi na wahalar aure, musamman wajen hada kayan aure dalilin tsadar rayuwa da ake ciki a wannan zamani.

A Arewacin Najeriya dai ana fama da matsalar yawaitar marasa aure da kuma yawan sake-saken aure da ake ta fuskanta tsakanin ma’aurata, wannan dalili ne ya sanya wata karamar hukuma a jihar Kano ta dauki matakin magance wannan matsaloli, musamman ma tsadar aure.

An hana hira da budurwa ba tare da ganawa da iyayenta ba

A wani rahoto da muka ci karo dashi a shafin yanar gizo na Dala FM Kano sun ruwaito cewa shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai ya rage farashin aure a fadin karamar hukumar.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa daga yanzu babu wani saurayi da zai sake kula budurwa, ba tare da yaje ya gana da iyayenta ba.

Aure tsakanin ango da amarya
Ango da Amarya | Photo Source: Bulama Cartoon

An sauke farashin aure a Dawakin Tofa

Dangane da batun kayan lefe kuwa, shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa an kayyade kayan zuwa akwati uku kacal.

Majalisar karamar hukumar ta Dawakin Tofa, ta sanya hannu a wannan sabuwar dokar, sakamakon shawarwari da tayi da masarautar Bichi, wanda a karshe majalisar ta kafa kwamiti ta musamman wacce za ta tabbatar da dokar.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na kananan hukumomin yankin, Sagir Abdullahi Kwanar Huguma, wacce ya raba ta ga manema labarai, ita ce ta bayyana haka.

Amarya ta damfari ango N10m ta gudu ta barshi ana saura kwana 10 daurin aure a Kaduna

An gurfanar da wata bazawara mai ‘yaya biyu, Fatima Sunusi, a gaban kotun majistire, dake zaune a unguwar Barnawa, cikin jihar Kaduna, bisa tuhumar ta da almundahana ga mijin da zata aura, wuri na gugar wuri har Naira miliyan goma, (N10,000,000) kwanaki goma kacal kafin daurin aurensu da shi.

Kamar yadda wakilin Dailly Trust ya bayyana, ya rage sauran kwanaki 10 kacal, wacce ake tuhumar ta auri angon nata mai suna Umar Oruma, wanda ya kai karar ta, sai tace ta fasa auren.

Ta koma ta sake auren tsohon mijinta

Kamar yadda Daily Trust din suka bincika, sun gano cewa, sai bayan da shirye-shiryen bikin su yayi nisa, sai wadda ake kara din ta canja shawara, inda ta koma ta auri mijinta na baya, wato uban ‘yayanta.

Wasikar sammacin kotu, ta nuna cewa da mai karar da ita wacce ake karar, sun fara soyayya ne tun a watan Yuni na shekara ta 2020. Sannan bayan sun dade suna soyayya, sai mai kara da wacce ake kara su kayi baiko a watan Janairun shekara ta 2021, kuma da yardar ita wadda ake karar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe