34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Gwamnatin jihar Neja ta kwace shanaye 500 daga hannun ‘yan bindiga, ta kuma yiwa iyalan sojoji wani kyakkyawan albishir

LabaraiGwamnatin jihar Neja ta kwace shanaye 500 daga hannun 'yan bindiga, ta kuma yiwa iyalan sojoji wani kyakkyawan albishir

Gwamnatin jihar Neja ta yi wani babban kamu a hannun ‘yan bindiga inda ta samu nasarar ƙwato waɗansu shanaye kimanin 500 a ƙauyukan Kuchi da Galadiman-kogo na yankunan Alawa da Elena a ƙananun hukumomin Shiroro da Munya na jihar.

Gwamnatin kuma tasha alwashin kula da iyalan sojojin da su ka rasa ran su wajen yaƙi da ‘yan ta’adda.

Kwamishinan kananan hukumomi na jihar ya ce gwamnan jihar na kokari wajen kawo karshen ta’addanci

Kwamishinan ƙananun hukumomi da tsaron cikin gida, Mr Emmanuel, shine ya bayyana hakan yayin da yake magana da ‘yan jarida kan halin da ake ciki dangane da tsaro da kuma ƙoƙarin da gwamnatin Abubakar Sani Bello ta ke yi wajen kawo ƙarshen ta’addancin da ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram ke yi a wasu sassa na jihar.

Gwamnatin jihar Neja ta kwace shanaye 500 daga hannun 'yan bindiga
Gwamnatin jihar Neja ta kwace shanaye 500 daga hannun ‘yan bindiga

Rundunar hadaka ce ta kwato shanayen

A cewar kwamishinan, ƙwato shanaye 300 da tumakai 100 da rundunar haɗaka ta tsaro tayi, ya samu nasara ne bayan samun wasu muhimman bayanan sirri waɗanda su ka taimaka wajen halaka ‘yan bindiga da dama da su ka addabi ƙauyuka a jihar.

Umar ya bayyana cewa wasu jami’an tsaro waɗanda bai faɗi yawan su ba sun riga mu gidan gaskiya a Shiroro da Munya. Sai dai ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ƙula da iyalan su saboda sadaukarwar da su ka nuna wajen kare martabar ƙasar nan.

‘Yan sanda sun ceto waɗanda ake yunkurin safarar su, sun dakile harin ‘yan bindiga a Katsina

Yan sanda sun ce an ceto mutanen da aka yi yunkurin safararsu daga yankin kudancin Najeriya a wani gari mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su tare da dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Fadimawa da ke karamar hukumar Kurfi a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai da yammacin ranar Juma’a, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa, ya ce an kuɓutar da wadanda aka yi safararsu daga yankin kudancin ƙasar ne a kauyen Koza da ke ƙaramar hukumar Mai’adua, mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.

“A yayin gudanar da bincike, wadanda lamarin ya rutsa da su sun bayyana cewa, wakilin su ne ya kawo su kauyen, inda suka ga tawagar ‘yan sandan, sai suka gudu da wayoyin su na GSM.

“Sannan kuma sun bayyana cewa suna kan hanyar su ne daga Najeriya zuwa Libiya ta kan iyakar Jamhuriyar Nijar. Ana ci gaba da bincike, za a mika su ofishin NAPTIP da ke Kano, domin ci gaba da bincike tare da damƙe ɓarayin,” yace.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe