29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

An kama wani katon gardi da yayi shigar mata yaje ya kashe dan gidan matar shi da wuka

LabaraiAn kama wani katon gardi da yayi shigar mata yaje ya kashe dan gidan matar shi da wuka

‘Yan sanda sun kama wani mutumi dan shekara 30, mai suna Shawn Bobb, wanda aka kama shi da hannu a kisan dan gidan matarshi a Guyana.

Helkwatar ‘yan sanda ta Guyana ta bayyana sun kama Bobb a gidan dake Helena dake lamba 1 a Mahaica, da misalin karfe 7 da minti 20, ranar Asabar 29 ga watan Janairu.

Yayi kokarin guduwa sanye da kayan mata

A lokacin da ‘yan sanda suka isa wajen, sun hango Bobb yana kokarin guduwa ta daya daga cikin tagogin gidan, inda yayi shiga irin ta mata, yayi kwalliya ya sanya gashin mata a kan shi.

A yanzu haka dai Bobb na hannun jami’an ‘yan sanda dake Georgetwon, inda suka kai shi asibiti domin duba lafiyar shi.

Bobb wanda yake aikin leburanci a East La Penitence Squatting Area, ya cakawa dan gidan matarshi mai shekaru 19 wuka a ranar 26 ga watan Janairun shekarar 2022.

Hukumar ‘yan sanda sun bayyana cewa yaron ya kamu da cutar COVID-19 bayan an garzaya da shi asibiti a Georgetown domin duba lafiyar shi kan raunin da Bobb yayi masa.

Yaron ya mutu a asibiti

Daga baya kuma aka kai shi cibiyar magance manyan cututtuka a Liliendaal, duka cikin garin na Georgetown, inda a nan ya mutu a ranar 27 ga watan Janairu.

A rahoton da ‘yan sanda suka fitar, yaron mai suna Edwards yayi kokarin kare mahaifiyar shi ne yayin da Bobb yake cin zarafin ta.

Bobb ya dauki wuka ya kaiwa mahaifiyar Edward hari saboda taki gama abinci da wuri.

Ita kanta matar bata tsira daga wajen Bobb ba domin kuwa ita ma ya caka mata wukar, inda aka garzaya da ita zuwa asibiti domin yi mata magani.

Na suma sa’adda matata ta ce ba ni ne mahaifin ’yar mu mai shekara 14 ba — Mahaifin ’ya’ya 4

Muridia da Yaqub Ganiyu sun shafe shekaru 17 suna zaune lafiya a matsayin ma’aurata, Allah ya albarkace su da yara hudu.

Abin baƙin ciki, zamantakewar tasu tana gab da rugujewa gaba ɗaya, saboda wani abin mamaki da Muridia ta yi na cewa Yaqub ba shine mahaifin ɗiyarsu mai shekara 14 ba.

Yaqub, wani direban babur ne wanda har yanzu bai fahimci gaskiyar iƙirarin da matarsa ​​ta yi ba, ya shaida wa Vanguard Metro cewa ya suma har sau biyu saboda ɗimauta lokacin da matarsa ​​ta ba da labarin.

A wata ziyara da ya kai gidansa mai daki daya a titin Matomi, Alagbado, garin da ke kan iyaka tsakanin jihohin Legas da Ogun, mahaifin ‘ya’yan hudu ya ce lamarin ya shafi matashin da ake magana a kai, da tausayawa, sannan kuma ya dagula zaman lafiya a gidansa.

A yanzu haka magidanta da matar suna zaune ne, wani mataki da Yakubu bai ji daɗinsa ba, saboda ya yi zargin cewa kungiyar ‘yan banga ta So-Safe Corps ta umurce shi da ya rika baiwa matarsa ​​Naira 5,000 duk mako domin kula da yara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe