36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Wasu ‘yan Arewa ne suka hana Jonathan kawo karshen Boko Haram lokacin mulkin shi – Tsohon Gwamna Babangida Aliyu

LabaraiWasu 'yan Arewa ne suka hana Jonathan kawo karshen Boko Haram lokacin mulkin shi - Tsohon Gwamna Babangida Aliyu

Tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu ya bayyana cewa wasu ‘yan Arewa ne suka hana tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kawo karshen kungiyar Boko Haram.

Ya zargi cewa wasu mutane ne daga Arewacin kasar suke hana Jonathan kawo karshen wannan yaki da yake da ‘yan ta’addar, saboda ra’ayinsu na siyasa, a wata hira da Babangida Aliyu ya yi Punch ya bayyana cewa babu dadin ji ko kadan ace an bar matsalar tsaro tayi karfi kamar haka.

‘Yar’adua da Jonathan sun fara daukar mataki kan Boko Haram – Babangida Aliyu

Tsohon gwamnan ya ce:

“A lokacin da Boko Haram ta fara, Umaru Musa Yar’adua da Goodluck Jonathan sune akan mulki, kuma sun fara daukan mataki kan lamarin, a karshe ya rage saura tsohon shugaban kasa Jonathan ya rage ya cigaba da aikin.

‘Yan Arewa da yawa sun hana Jonathan yin abinda ya kamata, saboda wani ra’ayinsu na siyasa, sun kawo wasu matsaloli da dama a lokacin da suka hana kawo karshen matsalar ta ‘yan ta’addar na Boko Haram, gashi kuma har yau muna tare da su.

“Matsalar ‘yan bindiga da mutane da dama suke ganin ba zai taba faruwa ba, har yanzu banji kowa yayi magana akan maganar Kawu Baraje ba, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, wanda ya bayyana cewa sun kawo masu tada kayar baya da kuma Fulani daga wasu wurare daban. Ina ganin a tunani na shine tsohon shugaban kasa Jonathan da bai basu mulki ba koda kuwa ace sune suka lashe zabe, amma kuma ya mika musu kujerar.

“Ya kira su yayi musu murna tun kafin a gama kirga kuri’u, inda a lokacin hakan ya kawo karshen duk wata manufar kawo wadannan mutane da za a yi amfani da su, kuma da na yi tunanin idan da gaske ne wadanda suka shigo da su za su biya su diyya su koma inda suk fito.

Tsohon Gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu
Tsohon Gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu

Da gwamnoni sunyi abinda ya kamata da yanzu babu matsalar tsaro

Babangida Aliyu ya bayyana cewa yayi imanin cewa, inda a ce gwamnoni sun yi abinda ya kamata daga shekarar 2015 zuwa yanzu, da tuni an manta da wata matsalar ‘yan bindiga.

Ya kara da cewa:

“A yau ya zama abin takaici a ce idan har ka bar gidanka a Abuja zaka je Kaduna, ko kuma daga Kaduna zaka je Abuja, sai dai ka fara Salati da Sallallami Allah ya raba ka da ‘yan bindiga, haka kuma abin ya shafi yawacin jihohin Arewa.

“Yanzu ko da rana tsaka, mutum ba zai iya bin hanyoyin mu ba cikin kwanciyar hankali. Saboda haka na tabbata cewa, gwamnoni ne kawai suke da ikon kawo karshen matsalar tsaro. Ina jin kunji lokacin da nake cewa shin 1 tafi 19 ne a Kano, duk da dai abubuwan sun canja, kowacce jiha daya daga cikin jihohi 19 muna da gwamna, amma duk da haka yanzu matsalolin karuwa suke yi fiye da dama.

‘Yan bindiga sun sace dan uwan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Wasu mutane ɗauke da bindigu sun sace ɗan’uwan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, a Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa.

Rahotanni sun nuna cewa an ɗauke Mr Robert Jepthan a daren ranar Talata a gidan sa da ke kan hanyar Dimrose, a yankin Biogbolo a birnin Yenagoa.

Yana tsaye a kofar gidan sa misalin ƙarfe 9:30 na dare, kwatsam wata mota ta tsaya kusa da shi sannan wasu mutane da su ka ɓoye fuskokin su, su ka ƙwamushe shi zuwa cikinta da ƙarfin tsiya.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce tuni ‘yan sanda su ka fara gudanar da bincike.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe