27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Ba zan iya kwatanta irin kaunar da al’umma ke nuna mini ba – Abba Kyari bayan shafe lokaci mai tsawo ba a ji duriyar shi ba

LabaraiBa zan iya kwatanta irin kaunar da al'umma ke nuna mini ba - Abba Kyari bayan shafe lokaci mai tsawo ba a ji duriyar shi ba

Jajirtaccen jami’in dan sandan nan, Abba Kyari, ya wallafa wasu sababbin hotuna a shafinsa na Facebook…

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (DCP) Abba Kyari, ya zama daya daga cikin mutanen da suka samu halartar daurin auren Maina Alkali, da a wajen shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa (IGP), a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Abba Kyari ya wallafa hotuna sama da 400 a Facebook

A jiya Asabar 29 ga watan Janairun shekarar 2022, Abba Kyari ya wallafa hotuna sama da guda 400 a shafinsa na Facebook, wanda ya dauka a wajen daurin auren, ciki kuwa hadda hoton da ya dauka da mai kudin nan Obi Cubana.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta ruwaito, wannann ya jawo kace-nace matuka a shafukan sadarwa sakamakon shi Abba Kyari da Obi Cubana idon kowa na kansu.

  • Super Cop 490x367 1
  • Super Cop 5 489x367 1
  • Super Cop 4 490x367 1
  • Super Cop 3 490x367 1
  • Super Cop 2 490x367 1
  • f32ef14cd54e920f

Abba Kyari dai an dakatar dashi daga aikin dan sanda, sakamakon zargin shi da hukumar ‘yan sandan kasar Amurka ta FBI ke yi masa da hannu a badakalar Abbas Ramoni, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Obi Cubana ya kwan hudu a hannun EFCC

Shi kuwa Obi Cubana hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ce ta kama shi ta tsare shi na tsawon kwanaki hudu sakamakon zargin shi da take da amfani da kudi ta hanyar da ba ta dace ba.

Haka kuma hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta sha kama shi da laifin hada kai da wasu manyan masu safarar miyagun kwayoyi na yankin nahiyar Asia.

Abba Kyari da Hushpuppi
DCP Abba Kyari da Abbas Ramoni Hushpuppi | Source: Facebook: Daily Trust

Sai dai a wajen daurin auren na dan gidan shugaban hukumar ‘yan sandan na kasa, an hango Abba Kyari da Obi Cubana suna musabaha.

Mutane na nuna mini tsananin kauna – Abba Kyari

Mutane da dama musamman a shafukan sada zumunta sun bukaci kwamitin bincike da ta bayyana sakamakon binciken da tayi kan Abba Kyari, kan zargin da FBI take yi masa.

Wannan sharhi da mutane ke yi ya cigaba da yaduwa, amma hakan bai hana jajirtaccen dan sandan wallafa sababbin hotunan ba, kuma ya ce ba zai iya kwatanta irin soyayyar da mutanen shi suke yi masa ba.

“Na kuma halarci daurin aure da dama a mahaifata ta Maiduguri jiya. Ba zan iya kwatanta irin tsantsar soyayyar da mutane na suke nuna mini ba. Muna godiya ga Allah,” ya rubuta.

Abba Kyari

Hukumar ‘yan sanda ta dakatar da Abba Kyari, ta bada dalili

Sa’o’i kadan bayan Babban Sufeto Janar na hukumar ‘yan sanda (IGP), Usman Baba, ya bukaci a dakatar da DCP Abba Kyari daga aikin hukumar ta ‘yann sanda, tuni har an yanke wannann hukunci an kuma dakatar dashi.

The News ta ruwaito hukumar ‘yan sandan Najeriya ta amince da dakatar da Abba Kyari daga aikin dan sanda a ranar Lahadi 1 ga watan Agusta, biyo bayan zargin da kotun kasar Amurka ke yi akan shi dangane da hannu a badakalar Hushpuppi.

Labarun Hausa sun gano cewa shugaban hukumar ‘yan sandan ya bukaci a dakatar da Kyari, sakamakon sunan shi da ya fito a cikin rahoton da hukumar FBI ta gabatar na cewa ya karbi cin hanci daga hannun fitaccen dan damfarar, akan ya kama daya daga cikin abokanan sana’ar shi.

Da yake tabbatar da dakatarwa da aka yiwa Kyari, kakakin rundunar ‘yan sandan, Ikechukwu Ani, ya ce Kyari ba zai cigaba da aiki ba har ya zuwa lokacin da za a kammala bincike akan shi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe