27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Lokaci ya yi da ya kamata ka bayyanawa al’umma wanda zai maye gurbinka – Gwamna ya bukaci shugaba Buhari

LabaraiLokaci ya yi da ya kamata ka bayyanawa al'umma wanda zai maye gurbinka - Gwamna ya bukaci shugaba Buhari

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari zai ba jam’iyyar APC shawara akan tsarin ta na karɓa-karɓa

Abiodun yayi nuni da cewa kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar ne zai fito da ɗan takarar da zai jagoranci jam’iyyar

Gwamnan ya ƙara da cewa shugaban ƙasar zai cigaba da baiwa jam’iyyar shawarwari domin samun nasara

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, a ranar Juma’a 28 ga watan Janairu, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai zama ɗan jagoran APC wajen tabbatar da adalci a tsarin ta na karba-karba.

Gwamna Abiodun ya faɗi hakan ne bayan shi da muƙarraban sa sun kai wa shugaba Buhari ziyarar godiya bayan ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a jihar.

Ya faɗa wa yan jaridar gidan gwamnati cewa, a matsayin sa na uba, shugaban ƙasar zai cigaba da bai wa jam’iyyar shawarwarin da za su kai ta gaci.

Gwamnan ya bayyana cewa a halin yanzu jam’iyyar APC ta na aiki akan wani tsari wanda za a bayyana wa mutane bayan ya samu amincewa daga kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta ƙasa.

A cewarsa, bayan sun amince ne za mu san daga yankin da shugaban ƙasar zai fito.

Babu adalci idan dan Arewa ya cigaba da rike kujerar shugaba Buhari a 2023 – Tanko Yakasai

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana ta tafka muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasar nan, game da batun karba-karba mulki a tsakanin ‘yan Arewa da ‘yan Kudu, musamman zaben 2023 me gabatowa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar; tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso; Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal; da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, na daga cikin ’yan siyasar Arewa da ke kai ma kujerar Buhari wawura.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe