27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Zan hana karuwanci a Abuja idan aka zaɓe ni – Cewar wani ɗan takara

LabaraiZan hana karuwanci a Abuja idan aka zaɓe ni - Cewar wani ɗan takara

Ɗan takarar kujerar ciyaman na Abuja Municipal a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, Chief Eric Ibe, ya sha alwashin hana karuwanci daga kan titunan babban birnin tarayya idan aka zaɓe shi.

Ya koka akan yadda mata da ƙananun yara 1,285 a birnin Abuja suke siyar da jikkunan su domin samun na abinci.

Ibe ya bayyana hakan ne yayin wata muhawara da aka shirya wa ‘yan takaran, wacce The Pink Vote Movement ta shirya kuma Wazobia FM ta watsa jiya a Abuja.

Dan takara
Zan hana karuwanci a Abuja idan aka zaɓe ni – Cewar wani ɗan takara

Ɗan takarar na SDP ya bayyana cewa:

“Mun gudanar da bincike inda mu ka samu cewa akwai kusan karuwai 1,285 mata da ƙananun yara da su ke yawo akan titunan Abuja kowanne dare. Wannan abin tsoro ne kuma abin takaici.

“Dole ne mu duba abinda zamu iya yi wajen ganin mun kawo ƙarshen hakan. Mutanen da mu ke magana akai ‘ya’yan mu da matan mu ne. Saboda haka dole ne mu yi abinda yakamata domin ganin mun cire su daga kan titiuna.

“A kan hakan ne muka kafa wasu ƙungiyoyin al’umma waɗanda a shirye suke da su haɗa hannu da gwamnati domin tabbatar da mun samarwa waɗannan matan rayuwa mai inganci.”

Ɗan takarar kuma yayi alƙawarin tafiyar da gwamnati wacce za ta ba kowa dama da kuma tallafi ga mata, inda yake cewa:

“Za mu tabbatar da cewa kaso 80% na dukkanin wasu muƙamai an baiwa mata saboda suna da ƙwarewa wajen gudanarwa sosai”

Tattara komatsanka ka bar gida na, Karuwancin ka ya yi yawa, Mai gidan haya ga dan haya

Wani mai gidan haya dan Najeriya ya ba wa wani matashi da ke haya a gidan takardar kora daga gidan.
Hakan ya biyo bayan yadda matashin ya ke karuwancinsa
yadda ya ga dama. Kuma ya ba shi takardan ne bayan ya ja kunnensa amma ya ki ya saurare shi.
Abin ya yi matukar ba ‘yan Najeriya da dama dariya inda su ka dinga tsokaci iri-iri akan takardar da mai gidan haya ya bayar.
Takardar ta bayyana a kafafen sada zumunta wanda shafin Gist Ville su ka wallafa a Facebook.
Wasikar an yi ta ne ga wani Babajide, sannan mai gidan haya ya kora bayani akan yadda ya dade ya na jan kunnen sa akan lalatar da ya ke yi amma ya ki ji.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe