27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

‘Yan sanda sun ceto waɗanda ake yunkurin safarar su, sun dakile harin ‘yan bindiga a Katsina

Labarai‘Yan sanda sun ceto waɗanda ake yunkurin safarar su, sun dakile harin ‘yan bindiga a Katsina

‘Yan sanda sun ce an ceto mutanen da aka yi yunkurin safararsu daga yankin kudancin Najeriya a wani gari mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su tare da dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Fadimawa da ke karamar hukumar Kurfi a jihar.

Kwalawa
‘Yan sanda sun ceto waɗanda ake yunkurin safarar su, sun dakile harin ‘yan bindiga a Katsina’

Da yake zantawa da manema labarai da yammacin ranar Juma’a, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa, ya ce an kuɓutar da wadanda aka yi safararsu daga yankin kudancin ƙasar ne a kauyen Koza da ke ƙaramar hukumar Mai’adua, mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.

“A yayin gudanar da bincike, wadanda lamarin ya rutsa da su sun bayyana cewa, wakilin su ne ya kawo su kauyen, inda suka ga tawagar ‘yan sandan, sai suka gudu da wayoyin su na GSM.

“Sannan kuma sun bayyana cewa suna kan hanyar su ne daga Najeriya zuwa Libiya ta kan iyakar Jamhuriyar Nijar. Ana ci gaba da bincike, za a mika su ofishin NAPTIP da ke Kano, domin ci gaba da bincike tare da damƙe ɓarayin,” yace.

Wadanda aka ceto sun hada da: Success Oshoopkeme, Isaac Debora, Amoruwa Ade, James Rebecca, Emmanuel Godwin, Zainab Tijjani, da Taofik Olawale.

‘Yan sanda sun yi magana kan harin Fadimawa


Dangane da harin ‘yan bindiga da aka dakile, Mista Isa, dan sanda reshen Kurfi “ya jagoranci tawagar jami’an da suka yi artabu da ‘yan ta’addan a wani artabu na tsawon sa’o’i.”

Mista Isa ya ce jami’an sun caje daji ne saboda ‘yan fashin da suka jikkata, bayan sun ƙwato musu dabbobin da suka sato.

‘Yan sanda sun kama wani matashi yana lalata da akuya a jihar Jigawa

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawan Shisu ya sanarwa da manema labarai cewa rundunar su ta samu nasarar cafke wani matashi dan shekara 25 a unguwar Kunnadi dake cikin karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa, yana lalata da akuya.

Jami’an ‘yan sandan sun samu nasarar cafke matashin ne a daidai lokacin da yake aikata masha’a da akuyar.

An ruwaito cewa saurayin ya kama akuyar da karfin tsiya ne ya fara lalata da ita har zuwa lokacin da jami’an tsaron suka iske shi turmi da tabarya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa tuni sun fara gudanar da bincike kan wannan lamari, kuma da zarar sun kammala hada bayanai akan binciken za su tisa keyarsa zuwa gaban kotu don ya girbi abinda ya shuka.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe