24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

‘Yar kwallo Musulma taki amincewa ta buga babban wasa bayan an bukaci ta tallata kungiyar ‘yan luwadi da madigo

Labarai'Yar kwallo Musulma taki amincewa ta buga babban wasa bayan an bukaci ta tallata kungiyar 'yan luwadi da madigo

Musulma ta farko da aka fara samu, a kungiyar kwallon hannu ta AFLW zata kauracewa cigaba da buga wasa a wannan shekara, saboda tsananin kishin addinin Musulunci da take yi.

Tauraruwar ta kulub din Western Sydney Giants, Haneen Zreika, ta kauracewa shiga zagayen wasan na wannan mako, sakamakon kin sanya riga mai nuni da goyon bayan LGBTQI (kungiyar ‘yan luwadi da madigo ) saboda ta yarda cewa addininta ya haramta goyon bayan irin wannan kungiya.

Ta sanar da shugabanninta dangane da matsayarta

An ruwaito cewa, budurwar ‘yar shekara 22 ta shaidawa ‘yan kungiyar wasan nasu ne dangane da matsayarta, inda kuma suka gamsu kuma suka mara mata baya.

Anyi kiyasin cewa, kimanin kashi 75 zuwa kashi 80 na gasar kungiyar AFLW duk na kungiyar LGBTQI dinne.

Zreika ta buga wasan da kungiyar ta AFLW tayi a shekarar 2021 da ta gabata, inda akayi wasanni kala-kala, da kuma magoya bayan bangarori da yawa, amma ‘yan kungiyar tasu basu sanya rigar ta LGBTQI mai dauke da alamar ‘yan luwadi da madigon ba.

Yar kwallo Musulma taki buga wasa
Wasu ‘yan wasan AFLW da suka amince suka sanya rigunan LGBTQI kenan

Yar kwallon na daya daga cikin gwarazan shekarar 2021

Ta fito a cikin hoton gwarazan wasannin a shekarar data gabata, amma a na wannan shekarar ta 2022, ba za ta fito ba.

Sauran yan kungiyar sun dukufa wajen sanya rigar ta LGBTQI, da kuma shirye-shiryen wasan, wanda za’a yi a Henson Park dake Marrickville ta tsakiyar yammacin birnin Sydney, a ranar Asabar.

Haka kuma, yan kungiyar suna sa ran zata halacci wajen wasan, harma tayi wasu ayyukan, koda ba za ta sanya rigar ba.

Ada yan Giant din sunki su bayyana dalilin matsayar ‘yar wasan, inda suka dinga yadawa a cikin gida cewa, ba za ta yi wasan bane saboda wasu dalilai na kashin kanta.

Zreika din tayi mahimmin aiki a kungiyar Western Sydney, nagartar da itace ke taimakon ta kuma take samun kariya hatta daga mahukuntan kungiyar.

Ta samu kyautar kwallon shekara a shekarar 2021

Yar shekara 22 ta ci kyautar kwallon shekara, a kakar gasa ta shekarar da ta gabata. Sannan ta wakilci Giant din a babbar gasar gudun zangon karshe.

Shugaban zauren majalisar Malaman addinin Musulunci na Victoria, ya gayawa The Age, cewa, abune mai mahimmanci da ta kauracewa wasan, indai tayi hakan ne domin tana ganin hakan ya sabawa addinin ta.

“Abu ne mai tsauri. Kasantuwar AFL yankine na hadakar mazauna, amma akwai girmama mabanbatan ra’ayoyi. Ina fata, kuma itama na tabbata tana fatan hakan, cewa da kungiyar wasan da kuma yan yankin AFL, duk zasu martaba matsayarta.”

An sauke ni daga mukamin Ministar Ingila saboda kasancewa ta Musulma, kuma nace Allah daya ne – Nusrat Ghani

Tsohuwar ministar sufuri ta Birtaniya, Nusrat Ghani, tace, takura mata akayi tilas ta sauka daga mukaminta, lokacin da akayi garan bawul a gwamnatin Birtaniya, a shekarar 2020, kawai dan ita Musulma ce.

A cewar yar jamiyyar ra’ayin rikau din (conservative ), kuma yar zauren majalisa; lokacin da tana hira da jaridar Sunday Times, a ranar Litinin.

Nusrat Ghani ta zama mace ta farko a cikin jami’an gwamnatin Birtaniya a shekarar 2018

A shekarar 2018 Nusrat Ghani ta zama mace ta farko a cikin kunshin jami’an gwamnatin Birtaniya. Ta zama ministar sufuri a gwamnatin, a karkashin babban minista, Theresa May.

Amma a watan Fabrairun shekarar 2020, sai aka fitar da Nusrat Ghani din daga jerin kunshin gwamnatin, yayin da sabon babban minista Boris Johnson ya kafa sabuwar gwamnati.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe