24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Mijina yana da damar ya auri mace fiye da ɗaya – Cewar Jaruma Mercy Aigbe bayan ta auri Musulmi

LabaraiAl'adaMijina yana da damar ya auri mace fiye da ɗaya – Cewar Jaruma Mercy Aigbe bayan ta auri Musulmi

Jarumar yarbawa mai cece-kuce Mercy Aigbe ta bayyana cewa sabon mijin ta mai shirya fina-finan yarbawa, Adeoti Kazim, Musulmi ne kuma ya na da hakkin ya auri mata fiye da ɗaya.

Jarumar mai shekaru 45 ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wani mai gabatar da shirin tattaunawa na TVC, Morayo Afolabi-Brown.

A cewar Alkur’ani, Musulunci ya kayyade namiji ga mata huɗu idan kawai zai iya yin adalci a tsakanin su.

Mijina yana da damar ya auri mata fiye da ɗaya – Mercy Aigbe
Mijina yana da damar ya auri mata fiye da ɗaya – Mercy Aigbe

Yayin da wannan shine karo na uku da Aigbe ta yi aure, shi ne auren Mista Kazim na biyu.

Mista Kazim ya na da ‘ya’ya huɗu yayin da matars a ta farko, Funsho, wacce ke zaune a Minnesota, Amurka, shahararriyar mai zane ce kuma mai kamfanin Asiwaju Couture.

Jarumar da sabon mijin ta sun yi bikin aure na sirri a Legas a jajiberin sabuwar shekara kuma sun bayyana labarin auren su a ranar Lahadi a kafar sada zumunta ta Instagram.

Wannan bayanin na zuwa ne kwana guda bayan da ta shaida wa Mrs. Afolabi-Brown, wacce ta shirya wani taron tattaunawa da aka fi sani da ‘Your View,’ cewa sabon mijin ta da tsohon mijinta, Lanre Gentry, ba abokan juna ba ne.

Jarumar ta auri Mista Gentry a shekarar 2013 kuma sun rabu a shekarar 2017. Auren ya samar da daya mai suna Juwon.

A ranar Laraba, Mrs. Afolabi-Brown ta tattauna batun sabon auren jarumar a yayin wasan kwaikwayon ta.

Ta sanar da cewa jarumar ta yi kokarin shiga cikin shirin, amma rashin kyawun siginar sadarwa ya sa ta kasa yin hakan.

Daga baya, Aigbe za ta aika da sakon ko ta kwana zuwa ga mai gabatar da shirin yana karantawa kai tsaye.

“Ina so kawai in bayyana ra’ayina, Adekaz ba abokin Lanre Gentry ba ne,” in ji sakon tes na ‘yar wasan.


Bayan cece-kuce da suka biyo bayan sanarwar ɗaurin auren, wannan ne karon farko da Aigbe ta fito fili ta yi magana kan auren nata da ya janyo cece-kuce.

A safiyar ranar Alhamis, Mrs. Afolabi-Brown ta tabbatar wa masu kallo cewa ta yi tattaunawa da fitacciyar jarumar a yammacin Laraba.

A tattaunawar da PREMIUM TIMES ta kiyaye, Mrs. Afolabi-Brown ta ce uwar ‘ya’yan biyun ta yi magana kan wasu batutuwan da suka shafi sabon auren ta.

Ta ce: _“Na yi magana da ita (Mercy) jiya da daddare, ta kira ni don in gyara wani tunani kuma ba daidai ba ne, Ta yaya za ta je ta auri babban aminin tsohon mijinta. Ta ce ba su taɓa zama abokai ba.”

Sun halarci wani taro ne kawai inda mijin ta na yanzu, dan kasuwa a masana’antar, ya gayyace ta zuwa bikin zagayowar ranar haihuwar sa, wanda ta halarta a kamfanin tsohon mijin ta.

Ta ce da ni “mutumin musulmi ne, ya na da hakkin ya auri mata fiye da daya, ya na da matsala da matar sa ta farko, kuma yanzu ya aure ta a matsayin matar sa ta biyu, ko mata ta biyu bata cancanci farin ciki ba? ”

Mai gabatar da shirin ta ce jarumar ta kuma bayyana cewa mutane sun rika aika mata da sakonnin batanci a shafin ta na Instagram wanda hakan ya bata mata rai da.

Tausayi ya sa an yiwa wata mata mai rainon marayu 3 kyautar gida sukutum, bayan an kore su a gidan haya

Wata mata, mai suna Suzanne Burke, ta yi wa kawarta mai suna Ebony Johnson gata, a lokacin da ta samu labarin cewa an kori kawarta daga gidan da take haya.

Suzanne ta ce ya kamata dole ta yi wani abu dan ganin ta ceto kawarta Ebony. Suzanne ta ce kawarta tana bukatar muhalli mai kyau inda zata zauna da ‘ya’yan ta.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe