24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Fasto ta bawa dalibai Musulmi da Kirista guda 60 kyautar dubu hamsin-hamsin saboda iyayen su basu da karfi

LabaraiFasto ta bawa dalibai Musulmi da Kirista guda 60 kyautar dubu hamsin-hamsin saboda iyayen su basu da karfi

Fitacciyar faston nan da ke zaune a Abuja, Prophetess, Rose Kelvin ta bai wa ɗalibai marasa galihu kiristoci da musulmi 60 kowannen su N50,000 don yin rijistar jarrabawar kammala sakandare ta 2022 (SSCE).

An zaɓo waɗanda suka ci gajiyar tallafin ne daga babban birnin tarayya Abuja. Rose Kelvin ta shaida wa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya jim kaɗan bayan gabatar da taron a ranar Laraba a Abuja, cewa ilimi shi ne jigo na rayuwa.

Fasto WAEC
Fasto bada kyautar N50,000 ga wasu dalibai 60 Kirista da Musulmai marasa galihu na SSCE

Yayin da jarabawar SSCE 2022 ke gabatowa, ɗalibai da dama a fadin kasar nan suna cikin fargaba, ba wai yadda za su yi nasara a jarabawarsu ba, sai dai fargabar rashin samun damar cin jarrabawar tare da abokan karatunsu saboda gazawar iyayen su ko marikan su wurin biya musu kudin WAEC.

“Na yi kira ga shuwagabannin Sakandare da ’yan kasuwa da yawa da su duba makarantun su su zabo ɗaliban da ba su da tabbacin zana jarabawar SSCE mai zuwa.

“Tare da bin diddigin ma’aikatan kafafen yada labarai na Ogwula, an zaɓo ɗaliban musulmi da kiristoci marasa galihu a ɗaruruwan makarantu daban-daban da ke lungu da sako na babban birnin tarayya Abuja domin cin gajiyar wannan tallafin.

“Na cika da mamaki, na kuma fashewa da kuka sosai a lokacin da nake sauraron wasu daliban da suka gamu da ajalin su, bayan da na mika wa kowannen su kudi Naira 50,000 domin su samu gurbin shiga makarantun su na gaba ta hanyar yin rajistar WAEC.

“Hakika, tushen itace yana da ɗaci, amma ‘ya’yan itacen suna da daɗi,” in ji annabiya Rose Kelvin. A halin da ake ciki, wasu daga cikin waɗanda suka ci moriyar a cikin wata hira sun yaba wa fasto Rose Kelvin don wannan karimcin.

Master Kingsley Usman, ɗaliban Sakandaren Gwamnati (GSS), Idu Koro, ya ce ba zai iya biyan kuɗin makarantar sa na ɗaya da na biyu ba saboda rashin kuɗi.

Wata wadda ta ci gajiyar shirin, Ms Winifred Agema, daga Benue kuma ɗiyar Jarumin da ya rasu a makarantar Sojan Najeriya a Makarantar Sakandare ta Day Army, Mogadishu Cantonment, ta gode wa Rose Kelvin “domin canja mata makomata.”
Ta ce mahaifiyar ta wadda bazawara ce kuma mai sayar da ayaba a Mararaba ta na kula da ita da ’yan’uwan ta shida, inda ta kara da cewa duk wani fata ya ɓata amma shugabar makarantar ta ba ta damar zuwa makaranta.

Falalat Idris, ɗaliba ce a makarantar akandaren Soja ta jeka ka dawo, Mogadishu, ta rasa mahaifiyar ta wadda ita ke kula da nauyin iyalin. mahaifinta talakan manomi ne wanda ya yi rashin lafiya bayan rasuwar matarsa ​​kuma a halin yanzu ya na kwance ba zai iya ciyar da iyalinsa ba.

Ba ta da wani zabi da ya wuce sayar da biredi don ta don tara kuɗin WAEC kafin shigowar Rose Kelvin rayuwar su. Yawancin waɗanda suka amfana sun gode mata don ba su sa ran rubuta 2022 SSCE ba.

An zabi dalibai 3 da Kwankwaso ya tura karatu a matsayin kwararrun masana kimiyya a duniya

Wata kwamatin nazari da bincike wacce farfesa John Loannidis na Jami’ar Sandford dake birnin California cikin kasar Amurka yake jagoranta, ya sanya dalibai guda uku da tsohon gwamnan Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya dauki nauyin su, a cikin jerin masana kimiyya a duniya wadanda aka fi ambato.

Daliban wadanda suka yi karatun digiri na biyu, Aliyu Isa Aliyu, Tukur Abdulkadir Sulaiman da kuma Abdullahi Yusuf suna cikin jerin wadanda suka ci gajiyar tallafin karatu zuwa kasashen waje, na gwamnatin Jihar Kano, a lokacin mulkin gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, daga shekara ta 2011 – 2014.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe