24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Kano: Shekarau ya bayyana sharuɗan yin sulhu da Ganduje

LabaraiKano: Shekarau ya bayyana sharuɗan yin sulhu da Ganduje

Sanatan da yake wakiltar Kano ta tsakiya kuma shugaban G7, Mallam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa a shirye ya ke da yayi sulhu da ɓangaren da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ke marawa baya na APC, amma a bisa sharaɗin yin adalci ga ‘yan jam’iyyar APC na Kano.

Shekarau ya bayyana hakan ne a wata hira da aka saki ranar Laraba a kan abinda ya wakana a wajen taron sasantawa da gwamnan jihar Yobe kuma shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya jagoranta.

Shekarau da Ganduje
Kano: Shekarau ya bayyana sharuɗan yin sulhu da Ganduje

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, kwamitin riƙon ƙwaryar na APC wanda ke ƙarƙashin jagorancin Mai Mala Buni da gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Abubakar, sun gana a Abuja a ranar Talata domin sasanta ɓangarorin biyu waɗanda ba sa ga maciji da juna a Kano.

A cewar Shekarau na jihar Kano, kwamitin ba ta fitar da matsaya ba bayan tattaunawar amma ta roƙi ɓangarorin biyu su haɗa kawunan su domin samun zaman lafiya a tsakanin su.

“Kwamitin sulhun ta gamsu da nasarar da muka samu a kotu da kuma halin da jam’iyya take ciki a yanzu.’’ a cewar sa

‘’Mun gaya wa kwamitin cewa a shirye mu ke da yin tattaunawar sulhu amma a bisa wasu sharuɗa. Sharuɗan su ne mutunta ‘yan jam’iyya da adalci ga kowa ta yadda za a kare wa kowa haƙƙin sa.

‘’Fafatawar da mu ke yi ba wai don mu kawo rabuwar kai ba ne ko rashin kunya ga wani, amma sai don mu tabbatar da an bai wa kowa dama.

“Allah maɗaukakin sarki ya tabbatar da sulhu alkhairi ne, amma dole ne mu zama masu taka-tsantsan, gaskiya da adalci wajen yin sa.’’

Kano: Yadda wata mata ta danna wa wuyan ta fasasshen gilashi wanda ya yi ajalin ta

Ana zargin wata mata ‘yar anguwar Sheka da ke karkashin karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano da kashe kan ta da kan ta.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana yadda wata mata ta yi amfani da fasasshen gilashi na taga wanda ta dadara wa wuyan ta har sai da ran ta ya fita daga jikinta.

An samu bayanai akan yadda ta gartsa wa mahaifin ta cizo sannan ta datse dan yatsan ta wanda dama ya ke ciwo kafin ta halaka kan ta.

Dan uwan matar, Muhammad Sanusi ya shaida yadda ‘yar uwar tasa kafin ta halaka kan ta da kan ta ta yi fama da ciwon dan karkare na yatsa wanda ya dinga yi mata zugi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe