27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Kalaman batanci da wani fitaccen Malamin Addinin Musulunci yayi ga Sayyadina Ali (RA) ya fusata al’ummar kasar Pakistan

LabaraiKalaman batanci da wani fitaccen Malamin Addinin Musulunci yayi ga Sayyadina Ali (RA) ya fusata al'ummar kasar Pakistan

Mufti Tariq Masood wani malamin addini a ƙasar Pakistan ya janyo cece-kuce a kafar sada zumunta bayan ya yi we wasu kalaman ɓatanci akan sayyidina Ali (RA).

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da malamin ya taɓa yin irin waɗannan kalaman. A baya, malamin ya sha yin kalamai ma su tsauri waɗanda suke janyo masa suka a wurin mutane.

Tuni mutane a kafar sada zumunta suka fara kira kan hukumomi da su ɗamke malamin kamar yadda ake yiwa sauran waɗanda suk yi kalaman ɓatanci.

Afsar Ali ya rubuta cewa:

“Wani malami mai ra’ayin riƙau ya yi amfani da munanan kalamai akan Hazrat Ali (as). Muna kira ga hukumomi da su ɗauki matakan gaggawa kafin rikicin addini ya ɓarke.”

Syed Asadullahi ya rubuta cewa:

“Duk wanda ya zagi sayyidina Ali, tamkar ya zage ni ne, faɗar annabi Muhammad (SAW)”

Sai dai akwai wasu mutane a kafar ta sada zumunta da suke goyon bayan kalaman da malamin yayi, amma yawancin mutane sun yi kira akan a damƙe malamin bisa waɗannan munanan kalaman da yayi.

Har ya zuwa yanzu dai hukumomi a ƙasar ta Pakistan ba su ɗauki matakin komai ba dangane lamarin.

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan wata musulmar da ta yi batanci ga Annabi (SAW) a ƙasar Pakistan

Wata kotu a ƙasar Pakistan ta yanke hukuncin kisa ga wata mata musulma bayan ta zagi annabi Muhammad (SAW) ta hanyar sanya wasu hotuna masu nuna ɓatanci kan fiyayyen halitta tare da ɗaya daga cikin matan sa.

Kotun mai zama a birnin Rawalpindi na arewacin Pakistan, ta yanke hukuncin kisan ne kan Aneeqa Ateeq ranar Laraba bisa dokokin ƙasar waɗanda su ka tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya yi batanci ga fiyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).

“Abubuwan ɓatancin waɗanda ake zargin ta da aikatawa sun hada da yin wata wallafa a WhatsApp da kuma tura saƙonni tare da zane-zanen ga wanda ya shigar da ƙara, inda yace sun yi muni a wajen musulmi” kamar yadda alƙali Adnan Mushtaq ya bayyana cikin hukuncin sa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe