24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Wani bawan Allah ya karbi addinin Musulunci saboda kallon shirin fim din Izzar So da yake yi

LabaraiKannywoodWani bawan Allah ya karbi addinin Musulunci saboda kallon shirin fim din Izzar So da yake yi

Fim din Izzar So ya sanya wani mutumi dan asalin jihar Cross Rivers ya karbi addinin Musulunci, yayin da mutane da yawa ke kushe ‘yan fim…

A yayin da mutane da dama suke yiwa ‘yan shirin fina-finan Hausa na Kannywood kallon mutane dake bata tarbiyya da kuma lalata al’ada, sai gashi an samu wani mutumi ya karbi addinin Musulunci sakamakon kallon fim da yake yi.

Wani rahoto da muka ci karo dashi a shafin Facebook na Kannywood, ya nuna yadda wani bawan Allah ya canja addini zuwa addinin Musulunci sakamakon kallon fim din Izzar So da yake yi.

Mutumin da aka bayyana sunan shi da John, ya fito tun daga karamar hukumar Idom dake cikin jihar Cross Rivers, domin ya karbi kalmar Shahada, inda daga baya ya canja sunan shi zuwa Umar.

A bidiyon da shafin na Kannywood ta wallafa an nuno mutumin tare da shahararren jarumin nan Lawal Ahmad da kuma wasu mutane a lokacin da ake karanta masa kalmar shahada yake biyawa, inda a kasan bidiyon aka yi rubutu kamar haka:

Izzar So
Izzar So

“Masha Allah A Yaune Mukayi Babban Kamu A Musulunci Inda Wannan Bawan Allah Ya Shiga Musulunci Saboda Kallon IZZAR SO Da Yakeyi, Tun Daga Cross river, idom Ikon Local Government Cross River Yanzu Haka Dai Ya Karbi Musulunci, Kuma Yanzu Haka Sunansa Ya koma Umar Daga John, Munayi Masa Addu a Allah Yasa Ya shigo Addinin musulunci A Sa a Allah Yasa Ya Amfane Shi, Amin.”

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance:

Shirin Izzar so dai shiri ne mai dogon zango da yake tashe a wannan lokaci, wanda jarumi Lawal Ahmad yake shiryawa.

A baya dai dama jarumi Falalu Dorayi ya taba yin wata magana da yake nuni da cewa akwai mutane da dama da suka karbi addnin Musulunci sakamakon kallon fim din Haussa da suke yi.

Sai dai wannan magana ta jarumin ta tada kura, inda mutane a shafukan sadarwa suka yi caa suke ganin wannan magana ta jarumin sam ba haka take ba, domin a ganin su, babu abinda jaruman suke yi idan ba bata tarbiyya da al’adar al’ummar Hausa da Musulmai ba.

Na dauki nauyin kula da marayu har na aurar da daya ba tare da kowa ya sani ba – Bello M Bello

A wata hira da kafar yada labarai ta DW Hausa tayi da jarumi Bello Mohammed Bello, ya bayyana cewa gwamnati ko wata kungiya ba ta biyan sa aikin wayar da kan matasa da yake yi.

Ya ce yana yin haka ne kawai domin sauke hakkin mutuntaka, inda a cikin hirar ya bayyana cewa har marayu ya raina guda uku suka girma a gaban shi har ya aurar da daya.

Ya ce marayun yana rike da su tun lokacin rikicin addinin da aka yi da Jos a shekarar dubu biyu da daya (2001), inda aka samu asarar rayuka da dama a lokacin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe