24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Kotu ta bada umarnin a kamo mata jarumi Sadiq Sani Sadiq kan zargin almundahana

LabaraiKannywoodKotu ta bada umarnin a kamo mata jarumi Sadiq Sani Sadiq kan zargin almundahana

A wani labari da muka ci karo dashi da jaridar Freedom Radio ta wallaafa, ya nuna cewa wata kotu a jihar Kano ta bada umarnin a kamo mata fitaccen jarumin kamfanin fina-finan Hausa na Kannywood, Sadiq Sani Sadiq.

Kotun ta shari’ar Musulunci dake zama a unguwar Hotoro, karkashin jagorancin Mai Shari’a Sagir Adamu ita ce ta bada umarnin Kamo Sadiq Sani Sadiq, sakamakon bijirewa umarninta da yayi.

Tun da farko dai, wani daraktan fim ne mai suna Aliyu Adamu Hanas, ya kai karar Sadiq Sani Sadiq sakamakon bashi kafin alkalamin kudin aikin shirin wasan kwaikwayon shi, kuma bai yi aikin ba, sannan kuma ake zargin ya hana shi kudin, wannan dalili ya sanya ya garzaya zuwa kotu domin rokon ta bi masa hakkin shi.

Kotun dai ta aikewa da jarumi Sadiq Sani Sadiq sammaci amma ba a same shi ba, daga baya ta bada umarnin a like masa takardar a gaban gidansa dake Tudun Yola, amma har ya zuwa lokacin da muke kawo muku rahoton bai bayyana a gabanta ba.

Sadiq Sani Sadiq
Sadiq Sani Sadiq

Wakilin Freedom Radio Aminu Abdu Baka Noma ya ruwaito cewa, mai karar yana neman tarar naira dubu tamanin (N80,000) a hannun Sadiq Sani Sadiq, haka kuma zai sake shigar da kara ta neman hakkinsa kan bata masa lokaci da kuma jawo masa asara sakamakon rashin halartar aikin shi da yayi.

Wannan rahoto dai yayi kama da irin shari’ar da aka kammala tsakanin jaruma Hafsat Idris da mai kamfanin UK Entertainment, inda shi ma ya zarge ta da kin zuwa tayi aiki kamar yadda suka tsadance , kuma ba ta biya shi kudin shi ba, wanda a karshe har aka dangana zuwa kotu. Sai kuma daga karshe jarumi Ali Nuhu ya sanya baki a cikin lamarin domin yin sasanci a tsakaninsu.

Bidiyon jarumi Sadiq Sani Sadiq yana rawar rashin daraja da wata ya karade ko ina

Jarumi Sadiq Sani Sadiq ya shayar da mutane da dama mamaki bayyan bayyanar wani bidiyonsa wanda M13 Novel suka wallafa a tashar su ta YouTube.

A bidiyon an ga jarumin sanye da wasu fararen kaya irin na zamani yana kwasar wani rawa na rashin mutunci tare da wata budurwa wacce ta sa itama fararen kaya ta zubo gashin doki har gadon bayanta.

Rawan da suka yi kamar zasu shiga jikin juna shine ya fi tayar wa kowa hankali musamman yadda aka san jarumin da aure da mutuncinsa.

An dauki bidiyon ne kamar a wani gidan wasa don yayin da suke kwasar rawar akwai ihu da jama’a suke yi musu don kara tunzurasu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe