24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Babban yaron Atiku Abubakar ya ajiye tafiyar Atiku ya koma jam’iyyar APC tare da dumbin magoya bayansa

LabaraiBabban yaron Atiku Abubakar ya ajiye tafiyar Atiku ya koma jam'iyyar APC tare da dumbin magoya bayansa
  • Wani yaron tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, dake jihar Yobe. Ya bar tafiyar Atiku ya koma APC
  • Muhammad Abdul Babangida, ya bar PDP tare da magoya bayansa, inda zasu koma APC a Arewa maso gabashin jihar
  • Babangida dai karamar hukumar su daya da gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni

Mataimakin shugaban hadinkan matasan jamiyyar PDP ta Arewa maso gabas, Muhammad Abdul Babangida, ya bar jamiyyar PDP shi da magoya bayansa, inda ya koma APC jamiyya mai ci, a jihar Yobe.

Jim kadan bayan ya fita, Babangida ya shaidawa jaridar Leadership cewa, jamiyyar PDP bata yi da shi da magoya bayansa.

Yace sun yanke shawarar fadawa jamiyya mai mulki ta APC, bayan ya tuntubi wasu daga cikin magoya bayansa.

Ya kara da cewa, ayyukan ci gaba da jamiyyar APC ta samar a fadin kasa baki daya, shine ya ja hankalin sa, shi da magoya bayansa suka koma cikinta.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar

Magoya bayan Atiku sun kara kaimi wajen nuna goyon baya gareshi a Twitter

A daidai wannan lokacin, magoya bayan Atiku sun dage da tallata shi gabanin babban zabe na 2023 mai karatowa.

Aliyu Yahya ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa:

“Babu katsalandan, babu waige, babu juya baya. Gaba dai gaba dai Atiku. Yan Nageriya sun dage, sun tsaya sun kudurce akan Atiku a shekarar 2023.

Marwan Yunusa ya rubuta cewa:

Ina tare da Atiku, a zaben 2023 saboda shi ginshiki ne ga kyakkyawan jagoranci.

SouthWest Yoruba for Atiku:

“Ya rubuta, ayyukan Atiku a baya, na gwazo, kwarewa, da kuma samar da abubuwa, su suke yi masa aiki.

An gargadi PDP akan baiwa dan Arewa takara a shekarar 2023

A wani labari makamancin wannan, An gargadi jamiyyar PDP akan baiwa dan Arewa takarar Shugaban kasa, a zaben shekarar 2023.

Wata kungiyar wayar da kai akan sha’anin siyasa Reset Nigeria, itace tayi kiran, a wani sako data fitar kuma suka aikawa Legit.ng, a ranar Litinin 14 ga watan Janairu.

Kungiyar tace jam’iyyar PDP zata yi asarar mabiya masu yawa idan ta kuskura, bata fitar da dan takarar shugaban kasa daga bangaren kudancin Najeriya ba. Kamar yadda yake a tsarin shugabancin kasa tsakanin kudu da Arewa.

2023 : Save Nageria movement sun soki muradin takarar Anyim da Wike

A nata bangaren, ita kuma kungiyar save Nigeria movement, sunyi fatali da muradin tsohon shugaban majalisar dattijai, Anyim pius Anyim.

Shugaban kungiyar, Rev Solomon Semaka, wanda ya gana da ‘yan jaridu ranar Litinin 10 ga watan Janairu, harilayau ya gwasale salon kamun ludayin gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, akan burinsa ga zaben 2023, inda yake zargin sa da cewa yana sone ya dora shugaban kasar iyamurai, ko kuma dan Arewa.

Kungiyar ta ja hankalin ‘yan Nageriya da suyi hankali da Wike da kuma Anyim din, domin a cewar ta, suna aikine tare domin cimma manufarsu ta son kai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe